Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
24 verses
11-3 Waɗannan su ne 'ya'yan Dawuda, maza, waɗanda aka haifa masa a Hebron.Amnon wanda Ahinowam Bayezreyeliya ta haifa masa.Kileyab wanda Abigail Bakarmeliya ta haifa masa.Absalom ɗan Ma'aka 'yar Talmai, Sarkin Geshur.Adonaija ɗan Haggit.Shefatiya wanda Abital ta haifa.Itireyam wanda Egla ta haifa.
2[...]
3[...]
4Dukansu shida an haife su ne a Hebron inda ya yi sarauta shekara bakwai da wata shida.Ya yi sarauta a Urushalima shekara talatin da uku.
5Waɗanda aka haifa masa a Urushalima, su ne Shimeya, da Shobab, da Natan, da Sulemanu, su huɗu ke nan waɗanda Bat-sheba 'yar Ammiyel ta haifa masa.
6Yana da waɗansu 'ya'ya kuma, su ne Ibhar, da Elishuwa da Elifelet,
7da Noga, da Nefeg, da Yafiya,
8da Elishama, da Eliyada, da kuma Elifelet, su tara ke nan.
9Waɗannan duka su ne 'ya'yan Dawuda, maza, banda 'ya'yan ƙwaraƙwarai. Tamar ita ce 'yar'uwarsu.
10Waɗannan su ne zuriyar Sulemanu, daga Rehobowam, sai Abaija, da Asa, da Yehoshafat,
11da Yoram, da Ahaziya, da Yowash,
12da Amaziya, da Azariya, da Yotam,
13da Ahaz, da Hezekiya da Manassa,
14da Amon, da Yosiya.
15'Ya'yan Yosiya, maza, su ne Yohenan ɗan farinsa, na biyu shi ne Eliyakim, na uku shi ne Zadakiya, na huɗu shi ne Yehowahaz,
16Eliyakim yana da 'ya'ya biyu maza, su ne Yekoniya, da Zadakiya.
17'Ya'yan Yekoniya wanda aka kama, su ne Sheyaltiyel,
18da Malkiram, da Fedaiya, da Shenazzar, da Yekamiya, da Hoshama, da Nedabiya.
19Fedaiya yana da 'ya'ya biyu maza, su ne Zarubabel da Shimai. 'Ya'yan Zarubabel, maza, su ne Meshullam, da Hananiya, da Shelomit 'yar'uwarsu,
20da Hashuba, da Ohel, da Berikiya, da Hasadiya, da Yushab-hesed, su biyar ke nan.
21'Ya'yan Hananiya, maza, su ne Felatiya, da Yeshaya, da 'ya'yan Refaya, maza, da 'ya'yan Arnan, maza, da 'ya'yan Obadiya, maza, da 'ya'yan Shekaniya, maza.
22Ɗan Shekaniya shi ne Shemaiya. 'Ya'yan Shemaiya, maza, su ne Hattush, da Igal, da Bariya da Neyariya, da Shafat, su shida ke nan.
23'Ya'yan Neyariya, maza, su ne Eliyehoyenai, da Hezekiya, da Azrikam, su uku ne nan.
24'Ya'yan Eliyehoyenai, maza, su ne Hodawiya, da Eliyashib, da Felaya, da Akkub, da Yohenan, da Dalaya, da Anani, su bakwai ke nan.