Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
14 verses
1Kowane babban firist, da yake an zaɓe shi ne daga cikin mutane, akan sa shi yă wakilci mutane ga al'amarin Allah, don yă miƙa sadakoki da kuma hadayu domin kawar da zunubai.
2Yă kuma zamana wanda zai iya tafiyar da jahilai da sangartattu a cikin salihanci, tun da yake rarrauna ne shi ta ko'ina.
3Saboda haka, wajibi ne yă miƙa hadayu, ba saboda kawar da zunuban jama'a kaɗai ba, har ma don nasa.
4Ba wanda zai kai kansa wannan matsayi mai girma, sai dai Allah ya yi kiransa ga haka, kamar yadda aka kirayi Haruna.
5Haka kuma, Almasihu, ba shi ya ɗaukaka kansa ya zama Babban Firist ba, sai dai wannan ne ya sa shi, wanda ya ce da shi,“Kai Ɗana ne,Ni Ubanka ne yau.”
6Kamar dai yadda a wani wuri kuma ya ce,“Kai firist ne na har abada,Kwatancin ɗabi'ar Malkisadik.”
7Almasihu, a lokacin zamansa a duniya, ya yi addu'o'i da roƙe- roƙe, tare da kuka mai tsanani, har da hawaye, ga wannan da yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa saurare shi saboda tsananin miƙa kansa.
8Ko da yake shi Ɗa ne, ya koyi biyayya ta wurin wuyar da ya sha,
9da ya kai ga kammala, sai ya zama tushen madawwamin ceto ga dukkan waɗanda suke masa biyayya,
10gama Allah yana kiransa Babban Firist, kwatancin ɗabi'ar Malkisadik.
11Muna da abu da yawa da za mu faɗa a game da shi kuwa, amma zai yi wuyar bayani, da yake basirarku ta dushe.
12Ko da yake kamar a yanzu kam, ai, ya kamata ku zama masu koyarwa, duk da haka, ashe, ba ku wuce wani ya sāke koya muku jigajigan farko na Maganar Allah ba, har ya zamana sai an ba ku nono, ba abinci mai tauri ba.
13Ai, duk wanda yake nono ne abincinsa, bai ƙware da maganar adalci ba, kamar jariri yake.
14Amma abinci mai tauri, ai, na manya ne, wato waɗanda hankalinsu ya horu yau da kullum, su rarrabe nagarta da mugunta.