Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
11 verses
1Mutane sun ce,“Zo, mu koma wurin Ubangiji,Gama shi ne ya yayyaga,Shi ne kuma zai warkar.Shi ne ya yi mana rauni,Shi ne kuma zai ɗaure raunin da maɗauri.
2Bayan kwana biyu zai rayar da mu.A rana ta uku kuwa zai tashe muMu yi zammanmu a gabansa.
3Mu nace domin mu san UbangijiZuwansa tabbatacce ne kamar wayewar gari.Zai zo wurinmu kamar ruwan sama,Kamar ruwan bazara da yake shayar da ƙasa.”
4Ubangiji ya ce, “Me zan yi da ke, ya Ifraimu?Me zan yi da ke, ya Yahuza?Ƙaunarku tana kama da ƙāsashi,Kamar kuma raɓar da take watsewa da wuri.
5Domin haka na sassare su ta wurin annabawansu,Na karkashe su da maganar bakina.Hukuntaina suna kama da hasken da yake ketowa.
6Gama ƙauna nake so, ba sadaka ba,Sanin Allah kuma fiye da hadayu na ƙonawa.
7“Amma sun ta da alkawarina kamar Adamu,Sun ci amanata.
8Gileyad gari ne na masu aikata mugunta.Tana da tabban jini.
9Kamar yadda mafasa sukan yi fakon mutum,Haka nan firistoci suka haɗa kansuDon su yi kisankai a hanyar Shekem,Ai, sun aikata mugayen abubuwa.
10Na ga abin banƙyama a cikin Isra'ila,Karuwancin Ifraimu yana wurin,Isra'ila ta ƙazantar da kanta.
11“Ku kuma, ya mutanen Yahuza, an shirya muku ranar girbi,A lokacin da zan mayar wa mutanena da dukiyarsu.”