Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
10 verses
1Hamada za ta yi farin ciki.Furanni za su hudo a ƙasa da ba ta da amfani.
2Hamada za ta raira waƙa da sowa don murna,Za ta zama kyakkyawa kamar Dutsen Lebanon,Da dausayi kamar filayen Karmel da Sharon.Kowa zai ga mafificiyar ɗaukakar Allah,Ya ga girmansa da ikonsa.
3Ku ƙarfafa hannuwan da suka gaji,Da gwiwoyin da suke fama da rashin ƙarfi.
4Ku faɗa wa dukan wanda ya karai, ku ce,“Ka ƙarfafa, kada kuwa ka ji tsoro!Allah yana zuwa domin ya kuɓutar da kai,Yana zuwa domin ya ɗauki fansa a kan abokan gābanka.”
5Makaho zai iya ganin gari,Kurma kuma zai iya ji.
6Gurgu zai yi tsalle ya yi rawa,Waɗanda ba su iya magana za su yi sowa don murna.Rafuffukan ruwa za su yi gudu a cikin hamada,
7Yashi mai ƙuna kuma zai zama tafki,Ƙeƙasasshiyar ƙasa kuma za ta cika da maɓuɓɓugai.Inda diloli suka yi zama,Ciyawar fadama da iwa za su tsiro.
8Za a yi babbar karauka a can,Za a kira ta, “Hanyar Tsarki.”Ba mai zunubi da zai taɓa bi ta wannan hanya,Ba wawayen da za su ruɗar da waɗanda suke tafiya can.
9Ba za a sami zakoki a can ba,Mugayen namomin jeji ba za su bi ta can ba.Waɗancan da Ubangiji ya fansarSu za su zo gida ta wannan hanya.
10Za su kai Urushalima da murna,Suna raira waƙa suna sowa don murna.Za su yi farin ciki har abada,Ba damuwa da ɓacin rai har abada.