Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
15 verses
1Urushalima, ki ƙarfafa, ki yi girma kuma!Birni mai tsarki na Allah,Ki yafa wa kanki jamali!Arna ba za su ƙara shiga ta ƙofofinki ba.
2Ki kakkaɓe kanki, ya Urushalima!Ki tashi daga cikin ƙura,Ki hau gadon sarautarki.Ki ɓaɓɓale sarƙoƙin da suke ɗaure da ke,Ke kamammiyar jama'ar Sihiyona!
3Ubangiji ya ce wa jama'arsa,“Ba a biya kuɗi domin a saye ku ba,Amma ga shi, kuka zama bayi.Ba za a biya kuɗin fansa domin a 'yantar da ku ba,Amma, ga shi, za a 'yantar da ku.
4Kuka taɓa zaman baƙuntaka a Masar,Daga baya Assuriyawa suka zalunce ku ba gaira ba dalili.
5Yanzu kuma, ga shi, yana faruwa a Babila,Kuka zama kamammu a can, ba gaira ba dalili.Su da suke mulkinku suna girmankai, suna fāriya,Suna ta nuna mini raini.
6Amma zuwa gaba za ku saniNi ne Allah, wanda na yi magana da ku.”
7Me ya fi wannan kyau?A ga manzo yana zuwa ta kan duwatsu,Ɗauke da albishir mai daɗi, labarin salama.Ya yi shelar nasara, ya ce wa Sihiyona,“Allahnki sarki ne!”
8Waɗanda suke tsaron birni suna sowa,Suna sowa tare saboda murna!Za su ga komowar Ubangiji a Sihiyona da idanunsu!
9Ku ɓarke da sowar murna,Ku kufan Urushalima!Ubangiji ya ta'azantar da jama'arsa,Ya fanshi birninsa.
10Ubangiji ya nuna ikonsa mai tsarki,Ya ceci jama'arsa,Dukan duniya kuwa ta gani.
11Ku fita, ku bar BabilaKu dukanku da kuke ɗauke da keɓaɓɓen kayan Ubangiji!Kada ku taɓa abin da aka hana,Ku kiyaye kanku da tsarki,Ku fita ku bar birnin.
12A wannan lokaci ba za ku bukaci ku fita da garaje ba,Ba za ku yi ƙoƙari ku tsere ba!Ubangiji Allah ne zai bishe ku,Ya kuma kiyaye ku ta kowane gefe.
13Ubangiji ya ce,“Bawana zai yi nasara a aikinsa,Zai zama babba, a kuwa girmama shi ƙwarai.
14Mutane da yawa suka gigice sa'ad da suka gan shi,Ya munana har ya fita kamannin mutum.
15Amma yanzu al'ummai da yawa za su yi mamaki a kansa,Sarakuna kuwa za su riƙe baki saboda mamaki.Za su gani su kuma fahimci abin da ba su taɓa sani ba.”