Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
17 verses
1Ya Ubangiji, kai adali ne sa'ad da na kawo ƙara a gare ka.Duk da haka zan bayyana ƙarata agabanka,Me ya sa mugaye suke arziki cikinharkarsu?Me ya sa dukan maciya amana sukezaman lafiya,Suna kuwa ci gaba?
2Kai ka dasa su, sun kuwa yi saiwa,Suna girma, suna kuma ba da'ya'ya,Sunanka na a cikin bakinsu, ammakana nesa da zuciyarsu.
3Amma kai, ya Ubangiji, kana sane dani, kana ganina,Kai kanka kake gwada tunanina.Ka jawo su kamar tumaki zuwamayanka,Ka ware su domin ranar yanka.
4Sai yaushe ƙasar za ta dainamakoki,Ciyawar kowace saura kuma ta dainayin yaushi?Saboda muguntar mazaunan ƙasarne dabbobi da tsuntsaye sukaƙare,Domin mutanen suna cewa, “Ba zaiga ƙarshenmu ba.”
5Ubangiji ya ce,“Idan kai da mutane kun yi tserenƙafa sun gajiyar da kai,Yaya za ka iya gāsa da dawakai?Idan ka fāɗi a lafiyayyiyar ƙasa,Ƙaƙa za ka yi a kurmin Urdun?
6Gama har da 'yan'uwanka da gidanmahaifinka,Sun ci amanarka,Suna binka da kuka,Kada ka gaskata su,Ko da yake suna faɗa makamaganganu masu daɗi.”
7Ubangiji ya ce,“Na bar jama'ata.Na rabu da gādona,Na ba da wanda raina yake ƙauna ahannun maƙiyansa.
8Abin gādona ya zama mini kamarzaki a cikin kurmi,Ya ta da murya gāba da ni,Domin haka na ƙi shi.
9Ashe, abin gadon nan nawa ya zamadabbare-dabbaren tsuntsun nan nemai cin nama?Tsuntsaye masu cin nama sun kewayeshi?Tafi, ka tattaro namomin jeji,Ka kawo su su ci.
10Makiyaya da yawa sun lalatar dagonar inabina.Sun tattake nawa rabo,Sun mai da nawa kyakkyawan rabokufai da hamada.
11Sun maishe shi kufai, ba kowa,Yana makoki a gare ni,Ƙasar duka an maishe ta kufai,Amma ba wanda zuciyarsa ta damu akan wannan.
12A kan dukan tsaunukan nan nahamadaMasu hallakarwa sun zo,Gama takobin Ubangiji yana ta kisaDaga wannan iyakar ƙasa zuwawaccan,Ba mahalukin da yake da salama.
13Sun shuka alkama, sun girbeƙayayuwa,Sun gajiyar da kansu, amma ba suamfana da kome ba.Za su sha kunya saboda abin da sukegirbe,Saboda zafin fushin Ubangiji.”
14Ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan mugayen maƙwabtan Isra'ila waɗanda suka taɓa gādon da ya ba jama'arsa Isra'ila su gada. “Saboda haka zan tumɓuke su daga cikin ƙasarsu. Zan kuma tumɓuke mutanen Yahuza daga cikinsu.
15Bayan na tumɓuke su kuma, zan sāke yi musu jinƙai, in komar da su, kowanne zuwa gādonsa.
16Zai zama kuwa, idan za su himmantu su koyi al'amuran jama'ata, su yi rantsuwa da sunana, su ce, ‘Da zatin Ubangiji,’ kamar yadda suka koya wa jama'ata yin rantsuwa da Ba'al, sa'an nan za a gina su a tsakiyar jama'ata.
17Amma idan wata al'umma za ta ƙi kasa kunne, to, sai in tumɓuke ta ɗungum, in hallaka ta, in ji Ubangiji.”