Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
40 verses
1Ubangiji ya ce, “Lokaci yana zuwa da zan zama Allah na dukan iyalan Isra'ila, za su kuwa zama jama'ata.”
2Haka Ubangiji ya ce, “Jama'ar dasuka tsere wa takobi,Sun sami alheri a cikin jeji,A sa'ad da Isra'ila suka nemihutawa.”
3Ubangiji ya bayyana gare ni tundaga nesa cewa,“Ya Isra'ila, budurwa!Na kusace ki da madawwamiyarƙaunata,Ba zan fasa amintacciyar ƙaunata agare ki ba.Zan sāke gina ki,Za ki kuwa ginu,Za ki ɗauki kayan kaɗe-kaɗe,Za ki shiga rawar masu murna.
4[...]
5Za ki sāke dasa gonar inabiA kan duwatsun Samariya,Masu dashe za su dasa,Za su mori 'ya'yan.
6Gama rana tana zuwa sa'ad da maitsaro zai yi kiraA ƙasar tudu ta Ifraimu, ya ce,‘Ku tashi mu haura zuwa SihiyonaZuwa wurin Ubangiji Allahnmu.’ ”
7Ga abin da Ubangiji ya ce,“Raira wa Yakubu waƙar farin cikida ƙarfi,Ku ta da murya saboda shugabanal'ummai,Ku yi shela, ku yi yabo, ku ce,‘Ya Ubangiji ka ceci jama'arka,Wato ringin mutanen Isra'ila,’
8Ga shi, zan fito da su daga ƙasararewa,Zan tattaro su daga manisantanwurare na duniya,Tare da su makafi da guragu,Da mace mai goyo da mai naƙuda,Za su komo nan a babbar ƙungiya.
9Da kuka za su komo.Da ta'aziyya zan bishe su, in komarda su,Zan sa su yi tafiya a gefen rafuffukanruwa,A kan miƙaƙƙiyar hanya, inda baza su yi tuntuɓe ba.Gama ni uba ne ga Isra'ila,Ifraimu kuwa ɗan farina ne.”
10“Ku ji maganar Ubangiji,Ya ku al'ummai,Ku yi shelarsa har a ƙasashen da sukenesa, na gāɓar teku.Ku ce, ‘Shi wanda ya warwatsaIsra'ila zai tattaro ta,Zai kiyaye ta kamar yadda makiyayiyakan kiyaye garkensa.’
11Gama Ubangiji ya fanshi Yakubu.Ya fanshe shi daga hannuwanwaɗanda suka fi ƙarfinsa.
12Za su zo su raira waƙa da ƙarfi,A bisa ƙwanƙolin Sihiyona,Za su yi annuri saboda alherinUbangiji,Saboda hatsi, da ruwan inabi, damai,Saboda 'ya'yan tumaki da na shanu.Rayuwarsu za ta zama kamarlambu,Ba za su ƙara yin yaushi ba.
13Sa'an nan 'yan mata za su yi rawada farin ciki,Samari da tsofaffi za su yi murna.Zan mai da makokinsu ya zamamurna,Zan ta'azantar da su, in ba su farinciki maimakon baƙin ciki.
14Zan yi wa ran firistoci biki dawadata,Jama'ata za su ƙoshi da alherina,Ni Ubangiji na faɗa.”
15Ga abin da Ubangiji ya ce,“An ji murya daga Rama,Muryar baƙin ciki da kuka mai zafi,Rahila tana kuka saboda 'ya'yanta,ba su.
16Ki yi shiru, ki daina kuka,Ki shafe hawaye daga idanunki.Za a sāka miki wahalarki,Za su komo daga ƙasar abokin gāba,Ni Ubangiji na faɗa.
17Akwai sa zuciya dominki a nangaba,Ni Ubangiji na faɗa.'Ya'yanki za su komo ƙasarsu.
18“Na ji Ifraimu yana baƙin ciki, yanacewa,‘Ka hore ni, na kuwa horu,Kamar ɗan maraƙin da ba shi dahoro,Ka komo da ni don in zama kamaryadda nake a dā,Gama kai ne Ubangiji Allahna.
19Gama na tuba saboda na rabu dakai,Bayan da aka ganar da ni, sai nasunkuyar da kai,Kunya ta kama ni, na gigice,Domin ina ɗauke da wulakancinƙuruciyata.’
20Ashe, Ifraimu ba ƙaunataccenɗana ba ne?Ashe, shi ba ɗan gaban goshina bane?A duk lokacin da na ambace shi akan muguntarsaNakan tuna da shi da ƙauna.Saboda na ƙwallafa zuciyata akansa,Hakika zan yi masa jinƙai, niUbangiji na faɗa.
21“Ki kafa wa kanki alamun hanya,Ki kafa wa kanki shaidu,Ki lura da gwadabe da kyau,Hanyar da kin bi, kin tafi.Ya budurwa Isra'ila, ki komo,Komo zuwa biranen nan naki.
22Har yaushe za ki yi ta shakka,Ya ke 'yar marar bangaskiya?Gama Ubangiji ya halitta sabon abua duniya,Mace ce za ta kāre namiji.”
23Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, “Nan gaba za su sāke yin magana a ƙasar Yahuza da biranenta a sa'ad da na mayar musu da dukiyarsu.“ ‘Ubangiji ya sa maka albarka,Ya wurin zaman adalci,Ya tsattsarkan tudu!’
24Yahuza kuwa da dukan biranenta za su zauna tare a can, da manoma, da makiyaya, da garkunansu.
25Gama zan biya bukatar waɗanda suka gaji, in wartsakar da waɗanda ransu ya yi yaushi.”
26Irmiya ya farka, ya ce, “Ina kuwa cikin barcina mai daɗi sai na farka na duba.”
27“Ni Ubangiji na ce, ga shi, zan sa mutane da dabbobi su cika ƙasashen Isra'ila da na Yahuza.
28Zai zama kamar yadda na lura da su don a tumɓuke su, a rushe su, a lalatar da su, a kawo musu masifa, haka kuma zan lura da su, a kuma dasa su, ni Ubangiji na faɗa.
29A waɗannan kwanaki ba za su ƙara cewa,“ ‘Ubanni suka ci 'ya'yan inabi masutsami,Haƙoran 'ya'ya suka mutu’ ba.
30Amma kowa zai mutu sabodazunubin kansa,Wanda ya ci inabi masu tsami,Shi ne haƙoransa za su mutu.”
31Ubangiji ya ce, “Ga shi, kwanaki suna zuwa da zan yi sabon alkawari da mutanen Isra'ila da na Yahuza.
32Ba irin wanda na yi da kakanninsu ba, sa'ad da na fito da su daga ƙasar Masar, alkawarin da suka karya, ko da yake ni Ubangijinsu ne, ni Ubangiji na faɗa.
33Amma wannan shi ne alkawarin da zan yi da mutanen Isra'ila bayan waɗancan kwanaki, ni Ubangiji na faɗa. Zan sa dokokina a cikinsu, zan rubuta su a zukatansu, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama jama'ata.
34Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa, ko ɗan'uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji’ ba, gama su duka za su san ni, tun daga ƙarami har zuwa babba. Zan gafarta musu laifofinsu, ba kuwa zan ƙara tunawa da zunubansu ba.”
35Haka Ubangiji ya ce,Shi wanda ya ba da rana ta haskakayini,Ya sa wata da taurari su ba da haskeda dare,Shi ne yakan dama teku, ya saraƙumanta su yi ruri,Sunansa Ubangiji Mai Runduna.
36“Idan dai wannan kafaffiyar ka'idata daina aiki a gabana,Ni Ubangiji na faɗa,To, ashe, zuriyar Isra'ila za ta dainazama al'umma a gabana ke nanhar abada.
37Idan a iya auna sammai a kuma iyabincike tushen duniya a ƙarƙas,To, ashe, zan watsar da dukanzuriyar Isra'ila ke nan sabodadukan abin da suka yi,Ni Ubangiji na faɗa.
38“Ga shi, kwanaki suna zuwa da za a sāke gina birnin domin Ubangiji, ni Ubangiji na faɗa, tun daga hasumiyar Hananel zuwa yamma, har zuwa Ƙofar Kan Kusurwa.
39Sa'an nan ma'aunin zai daɗa gaba, har ya kai tudun Gareb, sa'an nan ya nausa zuwa Gowa.
40Dukan filin kwarin gawawwaki da toka, da dukan filaye har zuwa rafin Kidron zuwa kan kusurwar Ƙofar Doki wajen gabas, za su zama mai tsarki ga Ubangiji. Ba za a ƙara tumɓuke shi ko a rushe shi ba har abada.”