Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
28 verses
1Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan sauran al'umma.
2Ya yi magana game da sojojin Fir'auna, Sarkin Masar, waɗanda suke a bakin Kogin Yufiretis a Karkemish, waɗanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya ci su da yaƙi a shekara ta huɗu ta sarautar Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza.
3Masarawa suka yi ihu, suka ce,“Ku shirya kutufani da garkuwa,Ku matso zuwa wurin yaƙi!
4Ku ɗaura wa dawakanku sirdi, kuhau!Ku tsaya a wurarenku da kwalkwalia ka!Ku wasa māsunku!Ku sa kayan yaƙi!”
5Ubangiji ya yi tambaya ya ce,“Me nake gani?Sun tsorata, suna ja da baya,An ci sojojinsu, suna gudu,Ba su waiwayen baya, akwai tsoro akowane sashi.”
6Masu saurin gudu ba za su tsere ba,Haka nan kuma jarumi,A arewa a gefen Kogin Yufiretis,Sun yi tuntuɓe, sun fādi.
7Wane ne wannan mai tashi kamarKogin Nilu,Kamar kogunan da ruwansu yakeambaliya?
8Masar tana tashi kamar Nilu,Kamar kogunan da ruwansu yakeambaliya.Masar ta ce, “Zan tashi, in rufeduniya,Zan hallaka birane da mazaunacikinsu.”
9Ku haura, ku dawakai,Ku yi sukuwar hauka, ku karusai!Bari sojoji su fito,Mutanen Habasha da Fut masuriƙon garkuwoyi,Da mutanen Lud, waɗanda suka iyariƙon baka.
10Wannan rana ta Ubangiji, Allah MaiRunduna ce,Ranar ɗaukar fansa ce don ya ramawa maƙiyansa.Takobi zai ci, ya ƙoshi,Ya kuma sha jininsu, ya ƙoshi,Gama Ubangiji Allah Mai Rundunazai hallaka maƙiyansa,A arewa, a bakin Kogin Yufiretis.
11Ku mutanen Masar, ku haura zuwaGileyadDon ku samo ganye!A banza kuke morar magunguna,Ba za ku warke ba.
12Kunyarku ta kai cikin sauranal'umma,Kukanku kuma ya cika duniya.Soja na faɗuwa bisa kan soja.Dukansu biyu sun faɗi tare.
13Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan zuwan Nebukadnezzar, Sarkin Babila, don ya yi yaƙi da ƙasar Masar.
14“Ku yi shelarsa cikin garuruwanMasar,Cikin Migdol, da Memfis, daTafanes,Ku ce, ‘Ku tsaya, ku yi shiri,Gama takobi yana cin waɗanda sukekewaye da ku!’
15Me ya sa gunkinka, Afis, ya fāɗi,Wato bijimi, gunkinka bai tsaya ba?Domin Ubangiji ya tunkuɗe shiƙasa!
16Sun yi ta fāɗuwa,Suna faɗuwa a kan juna,Sai suka ce, ‘Mu tashi mu komawurin mutanenmu,Zuwa ƙasar haihuwarmu, mu gududaga takobin azzalumi!’
17“Ku ba Fir'auna Sarkin Masarsabon suna,‘Mai yawan surutu, wanda bai rifcizarafi ba!’
18Ni wanda sunana Ubangiji MaiRunduna Sarki ne,Na rantse da raina, wani zai ɓullo,Kamar Tabor a cikin tsaunuka,Ko kuwa kamar Karmel a bakinteku.
19Ya ku mazaunan Masar,Ku shirya kayanku don zuwa bauta,Gama Memfis za ta lalace, ta zamakufai,Ba mai zama a ciki.
20“Masar kyakkyawar karsana ce,Amma bobuwa daga arewa ta aukarmata!
21Sojojin ijararta kamar 'yan maruƙane, masu yawan kitse,Sun ba da baya, sun gudu, ba sutsaya ba,Domin ranar masifarsu ta zo,Lokacin halakarsu ya yi.
22Masar tana gudu, tana huci kamarmaciji,Gama abokan gābanta suna zuwa daƙarfi,Za su faɗo mata da gatura kamarmasu saran itatuwa.
23Ni Ubangiji na ce, za su sarikurminta,Ko da yake ba su ƙirguwa,Gama suna da yawa kamar fara,Ba su lasaftuwa.
24Za a kunyatar da mutanen Masar,An bashe su a hannun mutanenarewa.”
25Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, “Ga shi, zan hukunta Amon na No, da Fir'auna, da Masar, tare da allolinta, da sarakunanta, wato Fir'auna, tare da waɗanda suke dogara gare shi.
26Zan bashe su a hannun waɗanda suke neman ransu, wato a hannun Nebukadnezzar, Sarkin Babila, da shugabanninsa. Daga baya kuma mutane za su zauna a Masar kamar dā. Ni Ubangiji na faɗa.
27“Ya bawana Yakubu, kada ka jitsoro,Kada ka firgita, ya Isra'ila.Gama zan cece ka daga ƙasa mainisa,Zan ceci zuriyarka daga ƙasarbautarsu.Yakubu zai komo, ya yi zamansa darai kwance,Ba wanda zai razanar da shi.
28Ni Ubangiji na ce,Kada ka ji tsoro, ya bawanaYakubu,Gama ina tare da kai.Zan hallaka dukan sauran al'ummasarai inda na kora ka.Amma ba zan hallaka ka sarai ba.Zan hukunta ka yadda ya kamata,Ba zan bar ka ba hukunci ba.”