Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
39 verses
1Wannan shi ne abin da Ubangiji ya faɗa akan Ammonawa,“Isra'ila ba shi da 'ya'ya ne?Ko kuwa ba shi da māgada ne?Me ya sa waɗanda suke bautar Milkomsuka mallaki inda Gad take zama,Suka zauna a garuruwanta?
2Domin haka lokaci yana zuwa,Sa'ad da zan sa mutanen garinRabba ta Ammon su ji busaryaƙi.Rabba za ta zama kufai,Za a ƙone ƙauyukanta da wuta,Sa'an nan Isra'ila zai mallakiwaɗanda suka mallake shi.Ni Ubangiji na faɗa.
3“Ki yi kuka, ya Heshbon, gama Ai tazama kufai!Ku yi kuka, ku mutanen Rabba, kusa tufafin makoki.Ku yi gudu, kuna kai da kawowa acikin garuka,Gama za a kai Milkom bauta tare dafiristocinsa da wakilansa.
4Me ya sa kuke taƙama daƙarfinku,Ƙarfinku da yake ƙarewa, ku mutanemarasa aminci?Kun dogara ga dukiyarku,Kuna cewa, ‘Wane ne zai iya gāba damu?’
5Ga shi, zan kawo muku razana dagawaɗanda suke kewaye da ku,Za a kore ku, kowane mutum zaikama gabansa,Ba wanda zai tattara 'yan gudunhijira.Ni Ubangiji Allah Mai Rundunana faɗa.
6“Amma daga baya zan saAmmonawa su wadata kuma,Ni Ubangiji na faɗa.”
7Ga abin da Ubangiji Mai Rundunaya faɗa a kan Edom,“Ba hikima kuma a cikin Teman?Shawara ta lalace a wurin masubasira?Hikima ta lalace ne?
8Ku mazaunan Dedan, ku juya, kugudu,Ku ɓuya cikin zurfafa,Gama zan kawo masifa a kan IsuwaA lokacin da zan hukunta shi,
9Idan masu tsinkar 'ya'yan inabi sunzo wurinkaBa za su rage abin kala ba?Idan kuma ɓarayi sun zo da dare,Za su ɗauki iyakacin abin da suke sokurum.
10Amma na tsiraita Isuwa sarai,Na buɗe wuraren ɓuyarsa,Har bai iya ɓoye kansa ba,An hallakar da mutanen IsuwaTare da 'yan'uwansa damaƙwabtansa,Ba wanda ya ragu.
11Ka bar marayunka, ni zan rayar dasu.Matanka da mazansu sun mutu,Sai su dogara gare ni.”
12Ubangiji ya ce, “Ga shi, waɗanda ba a shara'anta su ga shan ƙoƙon hukunci ba, za su sha shi, to, kai za ka kuɓuta? Ba za ka kuɓuta ba, amma lalle za ka sha shi!
13Gama ni Ubangiji na rantse da zatina, cewa Bozara za ta zama abar tsoro, da abar dariya, da kufai, da abar la'ana. Dukan garuruwanta za su zama kufai har abada.”
14Irmiya ya ce,“Na karɓi saƙo daga wurinUbangiji.An aiki jakada a cikin al'ummaicewa,‘Ku tattara kanku, ku zo ku yi gābada ita,Ku tasar mata da yaƙi!’
15Gama ga shi, zan maishe kiƙanƙanuwa cikin al'ummai,Abar raini a wurin mutane.
16Tsoronki da ake ji da girmankankisun ruɗe ki,Ke da kike zaune a kogon dutse, akan tsauni,Ko da yake kin yi gidanki can samakamar gaggafa,Duk da haka zan komar da ke ƙasa,Ni Ubangiji na faɗa.”
17Ubangiji ya ce, “Edom za ta lalace, duk wanda ya bi ta wurin zai gigice, ya yi tsaki saboda dukan masifunta.
18Abin da zai faru ga Edom zai zama daidai da abin da ya faru ga Saduma, da Gwamrata, da biranen da suke kusa da su, a lokacin da aka kaɓantar da su. Ba wanda zai zauna cikinta, ba wanda kuma zai yi zaman baƙunci a cikinta, ni Ubangiji na faɗa.
19Kamar yadda zaki yakan fito daga cikin kurmin Urdun, garin ya fāda wa babban garken tumaki, haka zan sa nan da nan su gudu daga gare ta. Zan naɗa wani wanda na zaɓa, gama wa yake kama da ni? Wa zai yi ƙarata? Ina makiyayin da ya isa ya yi gāba da ni?
20Domin haka, ku ji shirin da ni Ubangiji na yi wa Edom, da abin da nake nufin yi wa mazaunan Teman. Hakika za a tafi da su, har da ƙanana na garken tumaki, zan kuma sa wurin kiwonsu ya zama ƙeƙuwa saboda su.
21Amon fāɗuwarsu zai sa ƙasa ta girgiza, za a kuma ji muryar kukansu har a Bahar Maliya.
22Wani zai tashi da sauri, ya yi sama kamar gaggafa. Zai buɗe fikafikansa a kan Bozara. Zukatan sojojin Edom za su zama kamar zuciyar macen da take naƙuda.”
23Ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan Dimashƙu,“Hamat da Arfad sun gigice,Domin sun ji mugun labari,sun narke saboda yawan damuwa,Ba za su iya natsuwa ba.
24Dimashƙu ta yi halin ƙaƙa naka yi,Ta juya, ta gudu,Tsoro ya kama ta,Azaba da baƙin ciki sun kama takamar na naƙuda.
25Ƙaƙa aka manta da sanannen birni,Birnin da take cike da murna?
26A waccan rana samarinta za su fāɗi adandalinta.Za a hallaka sojojinta duka,Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
27Zan kuma sa wuta a garun Dimashƙu,Za ta kuwa cinye fādodinBen-hadad.”
28Ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan Kedar da sarakunan Hazor, waɗanda sarki Nebukadnezzar ya ci da yaƙi,“Ku tashi zuwa Kedar,Ku hallaka mutanen gabas.
29Za a kwashe alfarwansu dagarkunansu,Da labulan alfarwansu, da dukankayansu.Za a kuma tafi da raƙumansu,Za a gaya musu cewa, ‘Razana takewaye ku!’
30“Ku mazaunan Hazor, ku gudu zuwanesa,Ku ɓuya cikin zurfafa, ni Ubangiji nafaɗa,Gama Nebukadnezzar, SarkinBabila, ya shirya mukumaƙarƙashiya,Ya ƙulla mugun nufi game da ku.
31Ku tashi ku fāɗa wa al'ummar da takezama lami lafiya,Waɗanda ba su da ƙofofi ko ƙyamare,Suna zama su kaɗai.
32“Za a washe raƙumansu dagarkunan shanunsu ganima,Zan watsar da masu yin kwaskwasko'ina,Zan kuma kawo musu masifu dagakowace fuska,Ni Ubangiji na faɗa.
33Hazor za ta zama kufai har abada,wurin zaman diloli,Ba wanda zai zauna a ciki, ba wandakuma zai yi zaman baƙunci a wurin.”
34Maganar da Ubangiji ya yi wa annabi Irmiya a kan Elam a farkon sarautar Zadakiya Sarkin Yahuza.
35Ubangiji Mai Runduna ya ce,“Zan karya bakan Elam, indaƙarfinta yake.
36Zan sa iska ta hura a kan Elam dagakusurwoyi huɗu na samaniya.Za ta watsar da mutane ko'ina,Har ba ƙasar da za a rasa mutuminElam a ciki.
37Zan sa mutanen Elam su ji tsoronmaƙiyansu waɗanda suke nemanransu.Da zafin fushina zan kawo musumasifa,In sa a runtume su da takobi,Har in ƙare su duka,Ni Ubangiji na faɗa.
38Zan kafa gadon sarautata a Elam,Zan hallaka sarkinta dashugabanninta.
39Amma daga baya zan sa Elam kumata wadata.Ni Ubangiji na faɗa.”