Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
64 verses
1Ubangiji ya ce,“Ga shi, zan kawo iskar ɓarna akan BabilaDa mazaunan Kaldiya.
2Zan aika da masu casawa zuwaBabila, za su casa ta,Su bar ƙasarta kango.Za su kewaye ta a kowane sashiA wannan ranar masifa.
3Kada ku bar maharbi ya yi harbi dabakansa,Kada kuma ya sa kayan yaƙinsa,Kada ku rage samarinta,Ku hallaka dukan sojojinta.
4Za su fāɗi matattu a ƙasarKaldiyawa,Za a sassoke su a titunansu.”
5Allah na Isra'ila da Yahuza,Ubangiji Mai Runduna, bai yashesu ba,Ko da yake sun yi wa Mai Tsarki naIsra'ila zunubi.
6Ku gudu daga cikin Babila,Bari kowa ya ceci ransa,Kada a hallaka ku tare da ita,Gama a wannan lokaci Ubangiji zaisāka mata,Zai sāka mata bisa ga alhakinta.
7Babila ta zama ƙoƙon zinariya ahannun Ubangiji,Ta sa dukan duniya ta yi maye.Ƙasashen duniya sun sha ruwaninabinta, suka haukace.
8Farat ɗaya, Babila ta fāɗi, takakkarye,Ku yi kuka dominta!Ku samo mata magani domin azabarda take sha, watakila ta warke.
9Mun ba Babila magani, amma ba tawarke ba.Bari mu ƙyale ta, kowannenmu yakoma garinsu,Gama hukuncinta ya kai sammai, yayi tsawo har samaniya.
10Ubangiji ya baratar da mu a fili,Bari mu tafi mu yi shelar aikinUbangiji Allahnmu a cikinSihiyona.
11Ku wasa kibau, ku cikakwaruruwanku!Ubangiji ya ta da ruhun sarakunanMediyawa,Domin yana niyyar hallaka Babila.Gama Ubangiji zai yi ramuwasaboda Haikalinsa.
12Ku ta da tuta don a faɗa wa garunBabila,Ku ƙarfafa matsara,Ku sa su su yi tsaro,Ku kuma sa 'yan kwanto!Ga shi, Ubangiji ya yi niyya, ya kuwaaikataAbin da ya faɗa a kan mazaunanBabila.
13Ƙarshenki ya zo,Ke mai zama kusa da ruwa mai yawa,Mai yawan dukiya.Ajalinki ya auka.
14Ubangiji Mai Runduna ya rantse dazatinsa, ya ce,“Hakika zan cika Babila da mutanekamar fāra,Za su kuwa raira waƙar nasara akanta.”
15Ubangiji ne ya halicci ƙasa daikonsa,Ya kafa duniya da hikimarsa,Ya kuma shimfiɗa sammai dafahiminsa.
16Bisa ga umarninsa ruwan da yakesamaniya yakan yi ruri,Yakan sa gajimare su tashi dagaƙarshen duniya,Yakan sa walƙiya ta walƙata cikinruwan sama,Yakan sa iska ta haura daga cikintaskokinsa.
17Kowane ɗan adam wawa ne, mararilimi,Kowane maƙerin zinariya kuma zaisha kunya daga wurin gumakansa,Gama siffofinsa na ƙarya ne, banumfashi a cikinsu.
18Su marasa amfani ne, aikin ruɗarwane kawai,Za su lalace a lokacin da za ahukunta su.
19Amma wanda yake wajen Yakubu bahaka yake ba,Domin shi ne ya halicci dukan abu,Isra'ila kuwa abin mallakarsa ne,Ubangiji Mai Runduna ne sunansa.
20Ubangiji ya ce,“Kai ne guduma da kayan yaƙina,Da kai ne na farfasa ƙasashen duniya,Da kai ne na hallaka mulkoki.
21Da kai ne na karya doki da mahayinsa,
22Da kai ne na farfasa karusa da mahayinsa.Da kai ne na kakkarya mace da namiji,Da kai ne na kakkarya tsoho da saurayi,Da kai ne na kakkarya saurayi da budurwa,
23Da kai ne na kakkarya makiyayi da garkensa,Da kai ne na kakkarya manomada dawakan nomansa,Da kai ne na kakkarya masu mulkida shugabanni.”
24Ubangiji ya ce, “Zan sāka wa Babila da dukan mazaunan Kaldiya a ganin idanunku saboda dukan muguntar da suka aikata a Sihiyona.
25“Ga shi, ina gaba da kai, ya dutse maihallakarwa,Wanda ya hallaka duniya duka.Zan miƙa hannuna gāba da kai,Zan mirgino da ƙasa dagaƙwanƙolin dutse,Zan maishe ka ƙonannen dutse.
26Ba za a sami dutsen yin kusurwa, kona kafa harsashen gini a cikinka ba,Amma za ka zama marar amfani har abada.”
27Ku ta da tuta a duniya,Ku busa wa ƙasashen duniya ƙaho,Ku shirya ƙasashe don su yi yaƙi da ita,Ku kirawo mulkokin Ararat, da naMinni, da na Ashkenaz, su yi yaƙi da ita.Ku naɗa sarkin yaƙi wanda zaishugabanci yaƙin da za a yi da ita,Ku kawo dawakai kamar fāra.
28Ku shirya ƙasashe su yi yaƙi da ita,Sarakunan Mediyawa, da masumulkinsu, da shugabanninsu,Da kowace ƙasar da take ƙarƙashin mulkinsu.
29Duniya ta girgiza, tana makyarkyatasaboda azaba,Gama nufin Ubangiji na gāba daBabila ya tabbata,Nufinsa na mai da ƙasar Babilakufai, inda ba kowa.
30Sojojin Babila sun daina yaƙi, sunazaune a cikin kagaransu.Ƙarfinsu ya ƙare, sun zama mata,An sa wa wuraren zamanta wuta,An karya ƙyamaren ƙofofin garinta.
31Maguji yana biye da maguji a guje,Jakada yana biye da jakada,Don su faɗa wa Sarkin Babila, cewaan ci birninsa a kowane gefe.
32An ƙwace mashigaiAn ƙone fadamu da wuta,Sojoji sun gigice.
33Ni Ubangiji Mai Runduna, Allah naIsra'ila na ce,“Mutanen Babila sun zama kamardaɓen masussukaA lokacin da ake sussuka,Ba kuwa da daɗewa ba lokacin girbe ta zai zo.”
34Nebukadnezzar, Sarkin Babila, yacinye Urushalima,Ya ragargaza ta,Ya maishe ta kufai,Ya haɗiye ta kamar yadda dodonruwa yakan yi,Ya cika cikinsa da kayan marmarinta,Ya tatse ta sarai.
35Bari mutanen Sihiyona su ce,“Allah ya sa muguntar da mutanenBabila suka yi mana ta koma kansu!”Bari kuma mutanen Urushalima su ce,“Allah ya sa hakkin jininmu ya komakan Kaldiyawa!”
36Ubangiji ya ce,“Zan tsaya muku,Zan ɗaukar muku fansa,Zan sa tekunsu da maɓuɓɓugarsu su ƙafe.
37Babila za ta zama tarin juji, wurinzaman diloli,Abar ƙyama da abar ba'a, inda ba kowa.
38Mutanen Babila za su yi ruri kamarzakuna,Su yi gurnani kamar 'ya'yan zaki.
39Sa'ad da suke cike da haɗama zan yimusu biki,In sa su sha, su yi maye, su yi murna.Za su shiga barcin da ba za su farka ba.
40Zan kai su mayanka kamar 'yanraguna, da raguna, da bunsurai.
41“An ci Babila,Ita wadda duniya duka take yabo ancinye ta da yaƙi,Ta zama abar ƙyama ga sauran al'umma!
42Teku ta malalo a kan Babila,Raƙuman ruwa masu hauka sun rufe ta.
43Garuruwanta sun zama abin ƙyama,Ta zama hamada, inda ba ruwa,Ƙasar da ba mazauna,Ba kuma mutumin da zai ratsa ta cikinta.
44Zan hukunta Bel, gunkin Babila,Zan sa ya yi aman abin da ya haɗiye,Ƙasashen duniya ba za su ƙarabumbuntowa wurinsa ba.Garun Babila ya rushe!”
45“Ku fito daga cikinta, ya jama'ata,Kowa ya tsere da ransa daga zafinfushin Ubangiji.
46Kada zuciyarku ta yi suwu,Kada kuma ku ji tsoro sabodalabarin da ake ji a ƙasar,Labari na wannan shekara dabam,na wancan kuma dabam,A kan hargitsin da yake a ƙasar,Mai mulki ya tasar wa mai mulki.
47Saboda haka kwanaki suna zuwa,Sa'ad da zan hukunta gumakan Babila,Za a kunyatar da dukan ƙasar Babila,Dukan matattunta za su faɗi a tsakiyarta.
48Sa'an nan sama da duniya, da dukanabin da take cikinsu,Za su raira waƙar farin ciki,Domin masu hallakarwa daga arewada za su auko mata,Ni Ubangiji na faɗa.”
49Babila za ta fāɗi,Saboda mutanen Isra'ila da dukanmutanen duniya waɗanda ta kashe.
50Ku waɗanda kuka tsere wa takobi!Ku gudu! Kada ku tsaya!Ku tuna da Ubangiji a can nesa inda kuke,Ku kuma yi ta tunawa daUrushalima.
51Mun sha kunya saboda zargin da akeyi mana,Kunya ta rufe mu,Gama baƙi sun shiga tsarkakanwurare na Haikalin Ubangiji.
52“Domin haka kwanaki suna zuwa,”in ji Ubangiji,“Sa'ad da zan hukunta gumakanBabila, da dukan ƙasarta,Waɗanda aka yi wa rauni, za su yi nishi.
53Ko da Babila za ta hau samaniya,Ta gina kagara mai ƙarfi a can,Duk da haka zan aiki masuhallakarwa a kanta,Ni Ubangiji na faɗa.”
54Ku ji muryar kuka daga Babila,Da hargowar babbar hallakarwadaga ƙasar Kaldiyawa!
55Gama Ubangiji yana lalatar da Babila,Yana kuma sa ta kame bakinta na alfarma,Sojoji suna kutsawa kamar raƙuman ruwa,Suna ta da muryoyinsu.
56Gama mai hallakarwa ya auka wa Babila,An kama sojojinta,An kuma kakkarya bakunansu,Gama Ubangiji shi Allah ne, mai sakayya,Zai yi sakayya sosai.
57“Zan sa mahukuntanta, da masu hikimarta,Da masu mulkinta, da shugabanninta,Da sojojinta su sha su yi maye.Za su dinga yin barcin da ba za su farka ba,”In ji Sarkin, mai suna Ubangiji Mai Runduna.
58“Ni Ubangiji Mai Runduna, na ce,Za a baje garun nan na Babila mai fāɗiZa a kuma ƙone dogayenƙyamarenta da wuta.Mutane sun wahalar da kansu a banza.Sauran al'umma sun yi wahala kawaidomin wutar lalata.”
59Jawabin da annabi Irmiya ya ba Seraiya, ɗan Neriya, wato jikan Ma'aseya, lokacin da ya tafi tare da Zadakiya, Sarkin Yahuza, zuwa Babila a shekara ta huɗu ta mulkinsa. Seraiya shi ne shugaba mai lura da gidajen saukar baƙi.
60Irmiya ya rubuta a littafi dukan masifun da za su auko wa Babila, wato dukan wannan magana da aka rubuta a kan Babila.
61Irmiya kuwa ya ce wa Seraiya, “Lokacin da ka kai Babila, sai ka karanta dukan maganan nan.
62Ka kuma ce, ‘Ya Ubangiji, kai ne ka yi magana a kan wannan wuri, cewa za ka lalatar da shi, har ba abin da zai zauna a ciki, mutum ko dabba. Wurin zai zama kufai har abada.’
63Sa'ad da ka gama karanta wannan littafi, sai ka ɗaura wa littafin dutse, sa'an nan ka jefar da shi tsakiyar Kogin Yufiretis.
64Sa'an nan ka ce, ‘Haka Babila za ta nutse, ba za ta ƙara tashi ba saboda masifar da Ubangiji zai kawo mata.’ ”Wannan shi ne ƙarshen maganar Irmiya.