Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
20 verses
1Zofar ya amsa.
2“Ba wanda zai amsa dukan wannan surutu?Yawan magana yakan sa mutum ya zama daidai?
3Ayuba, kana tsammani ba za mu iya ba ka amsa ba?Kana tsammani maganganunka na ba'aZa su sa mu rasa abin da za mu mayar maka?
4Ka ɗauka duk abin da kake faɗa gaskiya ne,Ka kuma mai da kanka kai mai tsarki ne a gaban Allah.
5Da ma Allah zai amsa maka,Ya yi magana gāba da kai,
6Da ya faɗa maka hikima tana da fannoni da yawa.Akwai abubuwa waɗanda suka fi ƙarfin ganewar ɗan adam.Duba, Allah ya ƙyale wani ɓangare na laifinka.
7“Kana iya gane matuƙa da iyakarGirman Allah da na ikonsa?
8Sararin sama ba shi ne matuƙa a wurin Allah ba,Amma ga shi, yana can nesa da kai,Allah ya san lahira,Amma kai ba ka sani ba.
9Fāɗin girman Allah ya fi duniyaYa kuma fi teku fāɗi.
10Idan Allah ya kama ka ya gurfanar da kai gaban shari'a,Wa zai iya hana shi?
11Allah ya san irin mutanen da ba su da amfani,Domin yana ganin dukan mugayen ayyukansu.
12Idan dakikan mutane sa yi hikima,To, jakunan jeji ma sa yi irin hali na gida.
13“Ayuba, ka shirya zuciyarka,Ka ɗaga hannuwanka zuwa wurin Allah.
14Ka kawar da mugunta da kuskure daga gidanka.
15Sa'an nan ka sāke shan ɗamarar zaman duniya,Da ƙarfi da rashin tsoro.
16Duk wahalarka za ta gushe daga tunaninka,Kamar yadda rigyawa takan wuce, ba a ƙara tunawa da ita.
17Ranka zai yi haske fiye da hasken rana da tsakar rana.Kwanakin ranka mafiya duhuZa su yi haske kamar ketowar alfijir.
18Za ka yi zaman lafiya, cike da sa zuciya,Allah zai kiyaye ka, ya ba ka hutawa.
19Ba za ka ji tsoron kowane maƙiyi ba,Mutane da yawa za su nemi taimako daga gare ka.
20Amma mugaye za su dudduba ko'ina da fid da zuciya,Ba su da wata hanyar da za su kuɓuta.Sauraronsu kaɗai shi ne mutuwa.”