Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
6 verses
1Bildad ya amsa.
2“Allah mai iko ne, duka sai a ji tsoronsa,A samaniya yake tafiya da mulkinsa da salama.
3Akwai wanda zai iya ƙidaya mala'ikun da suke masa hidima?Akwai wurin da hasken Allah bai haskaka ba?
4Akwai wanda ya isa ya zama adali,Ko mai tsarki a gaban Allah?
5Hasken wata ba haske ba ne a gare shi,Ko taurari ma ba su da tsarki a gabansa.
6To, mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai.Me mutum ya daɗa a gaban Allah?”