Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
10 verses
1Sai Yunusa ya yi addu'a ga Ubangiji Allah a cikin cikin kifin,
2ya ce,“A cikin wahalata na yi kira gare ka,ya Ubangiji,Ka a kuwa amsa mini.Daga can cikin lahira na yi kira,Ka kuwa ji muryata.
3Ka jefa ni cikin zurfi,Can cikin tsakiyar teku,Inda igiyoyin ruwa suka kewaye ni,Kumfa da raƙuman ruwanka sukabi ta kaina.
4Na ce, an kore ni daga wurinka,Duk da haka zan sāke ganinHaikalinka mai tsarki.
5Ruwa ya sha kaina,Tekun ta rufe ni ɗungum.Tsire- tsiren teku suka naɗe kaina.
6Na tafi can ƙasa ƙarƙashin tussanduwatsu.Ƙasar da ƙofarta take rufe har abada,Amma ka fitar da ni daga cikinramin, ya Ubangiji Allahna.
7Sa'ad da na ji raina yana rabuwa dani,Sai na tuna da kai, ya Ubangiji.Addu'ata kuwa ta kai gare ka aHaikalinka tsattsarka.
8Su waɗanda suke yin sujada ga gumakamarasa amfaniSun daina yi maka biyayya.
9Amma ni zan raira yabbai gare ka,Zan miƙa maka sadaka,Zan cika wa'adin da na yi.Ceto daga wurin Ubangiji yake.”
10Ubangiji kuwa ya umarci kifin, kifin kuwa ya amayar da Yunusa a gaɓar teku.