Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
37 verses
1Yesu na fita daga Haikalin, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Malam, dubi irin duwatsun nan da gine-ginen nan!”
2Sai Yesu ya ce masa, “Ka ga manyan gine-ginen nan? Ba wani dutsen da za a bari nan a kan ɗan'uwansa, da ba za a baje shi ba.”
3Yana zaune a kan Dutsen Zaitun wanda yake kallon Haikalin sai Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, da Andarawas suka tambaye shi a keɓe suka ce.
4“Gaya mana yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Wace alama kuma za a gani sa'ad da suke shirin aukuwa?”
5Sai Yesu ya fara ce musu, “Ku kula fa kada kowa ya ɓad da ku.
6Mutane da yawa za su zo da sunana, suna cewa su ne ni, har su ɓad da mutane da yawa.
7In kuma kun jin labarin yaƙe-yaƙe da jita- jitarsu, kada hankalinku ya tashi. Lalle ne wannan ya auku, amma ƙarshen tukuna.
8Al'umma za ta tasar wa al'umma, mulki ya tasar wa mulki. Za a yi ta raurawar ƙasa a wurare dabam dabam, da kuma yunwa. Amma fa duk wannan masomin azaba ne tukuna.
9“Amma ku kula da kanku, don za su kai ku gaban majalisa, a kuma yi muku dūka a majami'u. Za a kuma kai ku gaban mahukunta da sarakuna saboda sunana, domin ku ba da shaida a gabansu.
10Amma lalle sai an fara yi wa dukan al'ummai bishara.
11Sa'ad da suka kai ku gaban shari'a suka miƙa ku, kada ku damu kan abin da za ku faɗa. Amma duk abin da aka yi muku baiwa da shi a lokacin nan, shi za ku faɗa, domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne.
12Ɗan'uwa zai ba da ɗan'uwansa a kashe shi, uba kuwa ɗansa. 'Ya'ya kuma za su tayar wa iyayensu har su sa a kashe su.
13Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har ƙarshe zai cetu.”
14“Sa'ad da kuka ga an kafa mummunan aikin saɓo mai banƙyama a wurin da bai kamata ba (mai karatu fa yă fahimta), to, sai waɗanda suke ƙasar Yahudiya su gudu su shiga duwatsu.
15Wanda yake kan soro kuma kada yă sauko yă shiga gida garin ɗaukar wani abu.
16Wanda yake gona kuma kada ya koma garin ɗaukar mayafinsa.
17Kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokaci!
18Ku yi addu'a kada abin nan ya auku da damuna.
19A lokacin nan za a yi wata matsananciyar wahala, irin wadda ba a taɓa yi ba tun farkon halittar da Allah ya yi, har ya zuwa yanzu, ba kuwa za a ƙara yi ba har abada.
20Da ba don Ubangiji ya taƙaita kwanakin nan ba, da ba ɗan adam ɗin da zai tsira. Amma sabili da zaɓaɓɓun nan da ya zaɓa, sai ya taƙaita kwanakin.
21To, a lokacin nan kowa ya ce muku, ‘Kun ga, ga Almasihu nan!’ ko, ‘Kun ga, ga shi can!’ kada ku yarda.
22Don almasihan ƙarya da annabawan ƙarya za su firfito, su nuna alamu da abubuwan al'ajabi, don su ɓad da ko da zaɓaɓɓu ma, in zai yiwu.
23Amma ku kula! Na dai gaya muku kome tun da wuri.”
24“Amma lokacin nan, wato bayan tsabar wahalan nan, za a duhunta rana, wata kuma ba zai yi haske ba.
25Taurari za su riƙa faɗawa daga sararin sama, za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama.
26A sa'an nan ne za a ga Ɗan Mutum na zuwa cikin gajimare, da iko mai girma da ɗaukaka.
27Sa'an nan zai aiko mala'ikunsa su tattaro zaɓaɓɓunsa daga gabas da yamma, kudu da arewa, wato daga iyakar duniya har ya zuwa iyakar sama.”
28“Ku yi koyi da itacen ɓaure. Da zarar rassansa sun fara sakuwa, suna toho, kun san damuna ta yi kusa ke nan.
29Haka kuma sa'ad da kuka ga waɗannan abubuwa na aukuwa, ku sani ya kusato, a bakin ƙofa ma yake,
30Hakika, ina gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba sai duk abubuwan nan sun auku.
31Sararin sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba.”
32“Amma fa wannan rana ko wannan sa'a ba wanda ya sani, ko mala'ikun da suke Sama, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai.
33Ku kula, ku zauna a faɗake, kuna addu'a, domin ba ku san sa'ar da lokacin zai yi ba.
34Kamar mutum ne mai tafiya, in ya bar gida ya wakilta yaransa, kowanne da aikinsa, ya kuma umarci mai jiran ƙofa ya zauna a faɗake.
35To, ku zauna a faɗake fa, don ba ku san lokacin da maigidan zai dawo ba, ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko da carar zakara ne, ko da safe ne,
36kada ya zo kwaram, ya samu kuna barci.
37Abin kuwa da na gaya muku, ina gaya wa kowa ne, shi ne ku zauna a faɗake.”