Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
38 verses
1A lokacin nan da wani taro mai yawan gaske ya sāke haɗuwa, ba su kuwa da abinci, sai ya kira almajiransa, ya ce musu,
2“Ina jin tausayin wannan taro, don yau kwanansu uku ke nan a guna, ba su da wani abinci.
3In kuwa na sallame su su tafi gida da yunwa haka, ai, za su kasa a hanya, ga shi kuwa, waɗansunsu sun fito nesa.”
4Sai almajiransa suka amsa masa suka ce, “Ina za a iya samun gurasar da za ta ciyar da mutanen nan a jeji haka?”
5Sai ya tambaye su, “Gurasa nawa gare ku?” Suka ce, “Bakwai.”
6Sai ya umarci taron su zauna a ƙasa. Da ya ɗauki gurasan nan bakwai, ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya yi ta ba almajiransa su kai wa taron, suka kuwa kakkai musu.
7Suna kuma da ƙananan kifaye kaɗan. Da ya yi wa Allah godiya, sai ya ce su ma a kai musu.
8Suka ci, suka ƙoshi, har suka ɗauki ragowar gutsattsarin, cike da manyan kwanduna bakwai.
9Mutanen kuwa sun yi wajen dubu huɗu. Sai ya sallame su.
10Nan da nan kuwa ya shiga jirgi da almajiransa, ya tafi ƙasar Dalmanuta.
11Farisiyawa suka zo suka fara muhawara da shi, suna nema ya nuna musu wata alama daga sama, don su gwada shi.
12Sai ya yi wata doguwar ajiyar zuciya, ya ce, “Don me mutanen zamanin nan suke neman ganin alama? Hakika, ina gaya muku, ba wata alamar da za a nuna wa mutanen wannan zamani.”
13Daga nan ya bar su, ya sāke shiga jirgi, ya haye wancan ƙetaren.
14Sun kuwa manta, ba su kawo gurasa ba, sai guda ɗaya ce kawai gare su a jirgin.
15Ya gargaɗe su ya ce, “Ku kula, ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Hirudus.”
16Suka yi magana da juna a kan ba su da gurasa.
17Da yake Yesu ya gane haka, sai ya ce musu, “Don me kuke zancen ba ku da gurasa? Ashe, har yanzu ba ku gane ba, ba ku kuma fahimta ba? Zuciyarku a taurare take?
18Kuna da idanu, ba kwa gani ne? Kuna da kunnuwa, ba kwa ji ne? Ba kwa kuma tunawa ne?
19Da na gutsuttsura wa mutum dubu biyar gurasan nan biyar, kwando nawa kuka ɗauka cike da gutsattsarin?” Suka ce masa, “Sha biyu.”
20“To, gurasa bakwai da na gutsuttsura wa mutum dubu huɗu fa? Manyan kwanduna nawa kuka ɗauka cike da gutsattsarin?” Suka ce masa, “Bakwai.”
21Sai ya ce musu, “To, har yanzu ba ku fahimta ba?”
22Suka iso Betsaida. Aka kawo masa wani makaho, aka roƙe shi ya taɓa shi.
23Ya kama hannun makahon, ya kai shi bayan gari. Da ya tofa yau a idanunsa, ya ɗora masa hannu, sai ya tambaye shi cewa, “Kana iya ganin wani abu?”
24Sai makahon ya ɗaga kai, ya ce, “Ina ganin mutane kam, amma kamar itatuwa nake ganinsu, suna yawo.”
25Sai ya sāke ɗora hannu a idanunsa. Makahon kuwa ya zura ido ƙwar, ya warke, ya ga kome garau.
26Sai Yesu ya sallame shi ya koma gida, ya ce, “Ko ƙauyen ma kada ka shiga.”
27Yesu ya tashi, da shi da almajiransa, ya shiga ƙauyukan Kaisariya Filibi. A hanya kuwa ya tambayi almajiransa, “Wa mutane suke cewa nake?”
28Suka ce masa, “Yahaya Maibaftisma, waɗansu kuwa, Iliya, waɗansu kuma, wani daga cikin annabawa.”
29Sai ya tambaye su, “Amma ku fa, wa kuke cewa nake?” Bitrus ya amsa masa ya ce, “Kai ne Almasihu.”
30Sai ya kwaɓe su kada su gaya wa kowa labarinsa.
31Ya fara koya musu, cewa lalle ne Ɗan Mutum ya sha wuya iri iri, shugabanni, da manyan firistoci, da malaman Attaura su ƙi shi, har a kashe shi, bayan kwana uku kuma ya tashi da rai.
32Ya ko faɗi wannan magana a sarari. Sai Bitrus ya ja shi waje ɗaya, ya fara tsawatar masa.
33Amma da Yesu ya waiwaya ya ga almajiransa, ya tsawata wa Bitrus ya ce, “Ka yi nesa da ni, Shaiɗan! Ba ka tattalin al'amuran Allah sai na mutane.”
34Ya kira taron tare da almajiransa, ya ce musu, “Duk mai son bina, sai yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa, yă bi ni.
35Duk mai son tattalin ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, saboda bishara kuma, tattalinsa ya yi.
36Me mutum ya amfana in ya sami duniya duka a bakin ransa?
37Me kuma mutum zai iya bayarwa ya fanshi ransa?
38Duk wanda zai ji kunyar shaida ni da maganata a wannan zamani na rashin amana da yawan zunubi, Ɗan Mutum ma zai ji kunyar shaida shi, sa'ad da ya zo da ɗaukakar Ubansa tare da mala'iku tsarkaka.”