Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
58 verses
11 A ran nan Yesu ya fita daga gidan, ya je ya zauna a bakin teku.
22 Taro masu yawan gaske suka haɗu a wurinsa, har ya kai shi ga shiga jirgi, ya zauna. Duk taron kuwa suka tsaya a bakin gaci.
33 Sai ya gaggaya musu abubuwa da yawa da misalai, ya ce, “Wani mai shuka ya je shuka.
44 Yana cikin yafa iri sai waɗansu ƙwayoyi suka faɗa a hanya, sai tsuntsaye suka zo suka tsince su.
55 Waɗansu kuma suka faɗa a wuri mai duwatsu inda ba ƙasa da yawa. Nan da nan sai suka tsiro saboda rashin zurfin ƙasa.
66 Da rana fa ta ɗaga, sai suka yanƙwane, da yake ba su da saiwa sosai, suka bushe.
77 Waɗansu kuma suka faɗa cikin ƙaya, sai ƙaya ta tashi ta sarƙe su.
88 Waɗansu kuma suka faɗa a ƙasa mai kyau, suka yi tsaba, waɗansu riɓi ɗari ɗari, waɗansu sittin sittin, waɗansu kuma talatin talatin.
99 Duk mai kunnen ji, yă ji.”
1010Sai almajiran suka zo, suka ce masa, “Me ya sa kake musu magana da misalai?”
1111 Ya amsa musu ya ce, “Ku kam, an yarda muku ku san asiran Mulkin Sama, amma su ba a ba su ba.
1212Domin mai abu akan ƙara wa, har ya yalwata. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.
1313 Shi ya sa nake musu magana da misalai, don ko sun duba ba sa gani, ko sun saurara ba sa ji, ba sa kuma fahimta.
1414 Lalle a kansu ne aka cika annabcin Ishaya cewa,“ ‘Za ku ji kam, amma ba za ku fahimta ba faufau,Za ku kuma gani, amma ba za ku gane ba faufau,
1515 Don zuciyar jama'ar nan ta yi kanta,Sun toshe kunnuwansu,Sun kuma runtse idanunsu,Don kada su gani da idanunsu,Su kuma ji da kunnuwansu,Su kuma fahimta a zuciyarsu,Har su juyo gare ni in warkar da su.’
1616“Albarka tā tabbata ga idanunku domin suna gani, da kuma kunnuwanku domin suna ji.
1717 Hakika, ina gaya muku, annabawa da adalai da yawa sun yi ɗokin ganin abin da kuke gani, amma ba su gani ba, su kuma ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.
1818 “To, ga ma'anar misalin mai shukar nan.
1919Wanda duk ya ji Maganar Mulki bai kuma fahimce ta ba, sai Mugun ya zo ya zăre abin da aka shuka a zuciyarsa. Wannan shi ne irin da ya faɗa a hanya.
2020 Wanda ya faɗa a wuri mai duwatsu kuwa, shi ne wanda da zarar ya ji Maganar Allah, sai ya karɓa da farin ciki.
2121 Amma kuwa ba shi da tushe, rashin ƙarƙo gare shi kuma, har in wani ƙunci ko tsanani ya faru saboda Maganar, sai ya yi tuntuɓe.
2222 Wanda ya faɗa cikin ƙaya kuwa, shi ne wanda ya ji Maganar, amma taraddadin duniya da jarabar dukiya sukan sarƙe Maganar, har ta zama marar amfani.
2323 Wanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa, shi ne wanda yake jin Maganar, ya kuma fahimce ta. Hakika shi ne mai yin amfani har ya yi albarka, wani riɓi ɗari, wani sittin, wani kuma talatin.”
2424 Ya kawo musu wani misali kuma, ya ce, “Za a kwatanta Mulkin Sama da mutumin da ya yafa iri mai kyau a gonarsa.
2525 Sa'ad da mutane suke barci, sai anokin gābansa ya je ya yafa irin wata ciyawa a cikin alkamar, ya tafi abinsa.
2626 Da shukar ta tashi, ta yi ƙwaya, sai ciyawar ta bayyana.
2727 Sai bayin maigidan suka zo, suka ce masa, ‘Maigida, ashe, ba kyakkyawan iri ka yafa a gonarka ba? To, ta yaya ke nan ta yi ciyawa?’
2828 Sai ya ce musu, ‘Wani magabci ne ya yi wannan aiki.’ Bayin suka ce masa, ‘To, kana so mu je mu cire mu tara ta?’
2929 Amma ya ce, ‘A'a, kada garin cire ciyawar ku tumɓuke har da alkamar ma.
3030 Ku bari su zauna tare har lokacin yanka. A lokacin yanka kuma zan gaya wa masu yankan su fara yanke ciyawar su tara, su ɗaure dami dami a ƙone, alkamar kuwa su taro ta su sa a taskata.’ ”
3131 Ya kawo musu wani misali, ya ce, “Mulkin Sama kamar ƙwayar mastad yake, wadda wani mutum ya je ya shuka a lambunsa.
3232 Ita ce mafi ƙanƙanta a cikin ƙwayoyi, amma in ta girma, sai ta fi duk sauran ganyaye, har ta zama itace, har ma tsuntsaye su zo su yi sheƙarsu a rassanta.”
3333 Ya kuma ba su wani misali, ya ce, “Mulkin Sama kamar yisti yake, wanda wata mace ta ɗauka ta cuɗe da mudu uku na garin alkama, har duk garin ya game da yistin.”
3434 Yesu ya gaya wa taro duk waɗannan abubuwa da misalai. Ba ya faɗa musu kome sai da misali.
3535Wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Ishaya ne cewa,“Zan yi magana da misalai,Zan sanar da abin da yake ɓoye tun farkon duniya.”
3636 Sai ya bar taron, ya shiga gida. Almajiransa kuma suka zo gare shi, suka ce, “Ka fassara mana misalin nan na ciyawa a gonar.”
3737 Ya amsa ya ce, “Mai yafa kyakkyawan irin nan, shi ne Ɗan Mutum.
3838 Gonar kuwa ita ce duniya, kyakkyawan irin nan, su ne 'ya'yan Mulkin Allah, ciyawar kuwa, 'ya'yan Mugun ne.
3939 Magabcin nan da ya yafa ta kuwa, Iblis ne. Lokacin yankan kuwa, ƙarshen duniya ne, masu yankan kuma, mala'iku ne.
4040 Kamar yadda ake tara ciyawa a ƙone ta, haka zai kasance a ƙarshen duniya.
4141 Ɗan Mutum zai aiko mala'ikunsa, za su tattaro duk masu sa mutane laifi, da kuma duk masu yin mugun aiki, su fitar da su daga Mulkinsa,
4242 su kuma jefa su cikin wuta mai ruruwa. Nan za su yi kuka da cizon haƙora.
4343 Sa'an nan ne masu adalci za su haskaka kamar rana a Mulkin Ubansu. Duk mai kunnen ji, yă ji.”
4444 “Mulkin Sama kamar dukiya yake da take binne a gona, wadda wani ya samu, ya sāke binnewa. Yana tsaka da murna tasa, sai ya je ya sayar da dukan mallaka tasa, ya sayi gonar.”
4545 “Har wa yau kuma Mulkin Sama kamar attajiri yake, mai neman lu'ulu'u masu daraja.
4646 Da ya sami lu'ulu'u ɗaya mai tamanin gaske, sai ya je ya sai da dukan mallaka tasa, ya saye shi.”
4747 “Har wa yau kuma Mulkin Sama kamar taru yake da aka jefa a teku, ya kamo kifi iri iri.
4848 Da ya cika, aka jawo shi gaci, aka zauna, aka tsince kyawawan kifi, aka zuba a goruna, munanan kuwa aka watsar.
4949 Haka zai kasance a ƙarshen duniya. Mala'iku za su fito, su ware mugaye daga masu adalci,
5050 su jefa su cikin wuta mai ruruwa. Nan za su yi kuka da cizon hakora.”
5151 “Kun fahimci duk wannan?” Suka ce masa, “I.”
5252Sai ya ce musu, “To, duk malamin Attaura da ya zama almajirin Mulkin Sama, kamar maigida yake, wanda ya ɗebo dukiya sabuwa da tsohuwa daga taskarsa.”
5353 Da Yesu ya gama waɗannan misalai, sai ya tashi daga nan.
5454 Da ya zo garinsu, ya koya musu a majami'arsu, har suka yi mamaki, suka ce, “Daga ina mutumin nan ya sami wannan hikima haka, da kuma mu'ujizan nan?
5555 Ashe, wannan ba ɗan masassaƙin nan ba ne? Uwa tasa ba sunanta Maryamu ba? 'Yan'uwansa kuwa ba su ne Yakubu, da Yusufu, da Saminu, da kuma Yahuza ba?
5656 'Yan'uwansa mata ba duk tare da mu suke ba? To a ina ne mutumin nan ya sami waɗannan abu duka?”
5757Sai suka yi tuntuɓe sabili da shi. Amma Yesu ya ce musu, “Ai, annabi ba ya rasa girma sai dai a garinsu da kuma a gidansu.”
5858 Bai kuma yi mu'ujizai masu yawa a can ba, saboda rashin bangaskiyarsu.