Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
51 verses
1Yesu ya fita Haikalin, yana cikin tafiya, sai almajiransa suka zo suka nuna masa gine-ginen Haikalin.
2Amma ya amsa musu ya ce, “Kun ga duk waɗannan ko? Hakika, ina gaya muku, ba wani dutsen da za a bari nan a kan ɗan'uwansa ba a baje shi ba.”
3Yana zaune a kan Dutsen Zaitun sai almajiransa suka zo wurinsa a kaɗaice, suka ce, “Gaya mana, yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Mece ce kuma alamar dawowarka, da ta ƙarewar zamani?”
4Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku kula fa kada kowa ya ɓad da ku,
5domin mutane da yawa za su zo da sunana, suna cewa, su ne Almasihu, har su ɓad da mutane da yawa.
6Za ku kuma riƙa jin labarin yaƙe-yaƙe da jitajitarsu. Kada fa hankalinku ya tashi, don lalle ne a yi haka, amma ƙarshen tukuna.
7Al'umma za ta tasar wa al'umma, mulki ya tasar wa mulki. Za a kuma yi yunwa da raurawar ƙasa a wurare dabam dabam.
8Amma fa duk wannan masomin azaba ne tukuna.
9“Sa'an nan za su bashe ku, a ƙuntata muku, su kuma kashe ku. Duk al'ummai za su ƙi ku saboda sunana.
10A sa'an nan da yawa za su yi tuntuɓe, su ci amanar juna, su kuma ƙi juna.
11Annabawan ƙarya da yawa za su firfito, su ɓad da mutane da yawa.
12Saboda kuma yaɗuwar mugun aiki, sai ƙaunar yawancin mutane ta yi sanyi.
13Amma duk wanda ya jure har ƙarshe, zai cetu.
14Za a kuma yi bisharar nan ta Mulkin Sama ko'ina a duniya domin shaida ga dukkan al'ummai. Sa'an nan kuma sai ƙarshen ya zo.”
15“Don haka sa'ad da kuka ga mummunan aikin saɓo mai banƙyama, wanda Annabi Daniyel ya faɗa, an tsai da shi a Wuri Mai Tsarki (mai karatu fa yă fahimta),
16to, sai waɗanda suke ƙasar Yahudiya su gudu su shiga duwatsu.
17Wanda yake soro, kada ya sauko garin ɗaukar wanda yake a gidansa.
18Wanda yake a gona kuma, kada ya koma garin ɗaukar mayafinsa.
19Kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokaci!
20Ku yi addu'a kada gudunku ya zo da damuna, ko ran Asabar.
21A lokacin nan za a yi wata matsananciyar wahala, irin wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu, ba kuwa za a ƙara yi ba har abada.
22Ba don an taƙaita kwanakin nan ba, da ba ɗan adam ɗin da zai tsira. Amma sabili da zaɓaɓɓun nan za a taƙaita kwanakin.
23A sa'an nan kowa ya ce muku, ‘Kun ga, ga Almasihu nan!’ ko, ‘Ga shi can!’ kada ku yarda.
24Don almasihan ƙarya da annabawan ƙarya za su firfito, su nuna manyan alamu da abubuwan al'ajabi, don su ɓad da ko da zaɓaɓɓu ma in dai zai yiwu.
25To, na dai gaya muku tun da wuri.
26Saboda haka in sun ce da ku, ‘Ga shi can a jeji,’ kada ku fita. In kuwa sun ce, ‘Yana can cikin lolloki,’ kada ku yarda.
27Kamar yadda walƙiya take wulgawa walai daga gabas zuwa yamma, haka komowar Ɗan Mutum za ta zama.
28Inda mushe yake, ai, a nan ungulai sukan taru.
29“Bayan tsabar wahalar nan, nan da nan sai a duhunta rana, wata kuma ba zai yi haske ba. Taurari kuma za su farfaɗo daga sararin sama, za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke sararin sama.
30A sa'an nan ne alamar Ɗan Mutum za ta bayyana a sararin sama, duk kabilan duniya kuma za su yi kuka, za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gajimare, da iko da ɗaukaka mai yawa.
31Zai kuwa aiko mala'ikunsa su busa ƙaho mai tsananin ƙara, su kuma tattaro zaɓaɓɓunsa daga gabas da yamma, kudu da arewa, wato, daga wannan bangon duniya zuwa wancan.”
32“Ku yi koyi da itacen ɓaure. Da zarar rassansa sun fara sakuwa, suna toho, kun san damuna ta yi kusa ke nan.
33Haka kuma in kun ga duk waɗannan abubuwa, ku sani ya kusato, a bakin ƙofa ma yake.
34Hakika, ina gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba sai duk abubuwan nan sun auku.
35Sararin sama da kasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba.”
36“Amma fa wannan rana da wannan sa'a ba wanda ya sani, ko mala'ikun da yake Sama, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai.
37Kamar yadda aka yi a zamanin Nuhu, haka dawowar Ɗan Mutum za ta zama.
38Kamar a kwanakin nan ne gabannin Ruwan Tsufana, ana ci, ana sha, ana aure, ana aurarwa, har ya zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi,
39ba su farga ba har Ruwan Tsufana ya zo ya share su. Haka komowar Ɗan Mutum za ta zama.
40A sa'an nan za a ga mutum biyu a gona, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya.
41Za a ga mata biyu suna niƙa, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya.
42To, ku zauna a faɗake fa, don ba ku san ranar da Ubangijinku zai dawo ba.
43Amma dai ku sani, da maigida zai san ko a wane lokaci ne da dare ɓarawo zai zo, da ya zauna a faɗake ya hana a shigar masa gida.
44Don haka ku ma sai ku zauna a kan shiri, domin a lokacin da ba ku zata ba, Ɗan Mutum zai zo.”
45“Wane ne amintaccen bawan nan mai hikima, da ubangidansa ya ba shi riƙon gidansa, yă riƙa ba su abincinsu a kan kari?
46Albarka tā tabbata ga bawan da in ubangidansa ya dawo zai samu yana yin haka.
47Hakika, ina gaya muku, sai ya ɗora shi a kan dukan mallakarsa.
48Amma in bawan nan mugu ne, ya kuma ce a ransa, ‘Ubangidana ya jinkirta zuwansa,’
49sa'an nan ya soma dūkan abokan bautarsa, yana ci yana sha tare da mashaya,
50ai, ubangidan wannan bawa zai zo a ranar da bai zata ba, a kuma lokacin da bai sani ba,
51yă farfasa masa jiki da bulala, ya ba shi rabonsa tare da munafukai. Nan za a yi kuka da cizon baki.”