Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
16 verses
1Ubangiji ya yi magana da Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da na Hezekiya, sarakunan Yahuza. Ya yi masa magana a kan Samariya da Urushalima.
2Dukanku ku ji, ku al'ummai!Ki kasa kunne, ya duniya, da dukanabin da yake cikinki.Bari Ubangiji AllahDaga Haikalinsa mai tsarki ya zamashaida a kanku.
3Ga shi, Ubangiji yana fitowa dagawurin zamansa,Zai sauko, ya taka kan tsawawanduwatsun duniya.
4Duwatsu za su narke a ƙarƙashinsa,Kwaruruka za su tsattsage kamarkakin zuma a gaban wuta,Kamar ruwa yana gangarowa dagatsauni.
5Duk wannan kuwa saboda laifinYakubu ne,Da laifin Isra'ila.Mene ne laifin Yakubu?Ashe, ba bautar gumaka da zaluncinda ake yi a Samariya ba?Mene ne kuma laifin Yahuza?Ashe, ba bautar gumaka da zaluncinda ake yi a Urushalima ba?
6“Domin haka zan mai da Samariyajujin kufai a karkara,Wurin dasa kurangar inabi.Zan zubar da duwatsunta a cikinkwari,In tone harsashin gininta.
7Za a farfashe dukan siffofinta nazubi,Za a ƙaƙƙone dukiyarta da wuta,Zan lalatar da gumakanta duka,Gama ta wurin karuwanci ta samosu,Ga karuwanci kuma za su koma.”
8Mika ya ce, “Saboda wannan zan yibaƙin ciki, in yi kuka,Zan tuɓe, in yi tafiya huntu.Zan yi kuka kamar diloli,In yi baƙin ciki kamar jiminai.
9Gama raunin Samariya, ba yawarkuwa,Gama ya kai Yahuza,Ya kuma kai ƙofar jama'ata aUrushalima.”
10Kada a faɗe shi a Gat,Sam, kada a yi kuka.Yi birgima cikin ƙura a Bet-leyafra.
11Ku mazaunan Shafir, ku wuceabinku da tsiraici da kunya.Mazaunan Za'anan ba su tsira ba.Bet-ezel ta yi kururuwa, “Zaitumɓuke harasashin gininki.”
12Mutanen Marot sun ƙosa su gaalheri,Amma masifa ta zo ƙofarUrushalima daga wurin Ubangiji.
13Ku mutanen Lakish, ku ɗaura wadawakai karusai,Gama ku kuka fara yin zunubi aSihiyona,Gama an iske laifofin Isra'ilacikinku.
14Domin haka sai ku ba Moreshet-gatguzuri,Mutanen Akzib za su yaudarisarakunan Isra'ila.
15Ku mazaunan Maresha, Ubangiji zaikawo wanda zai ci ku da yaƙi,Darajar Isra'ila za ta shigaAdullam.
16Ku aske kanku saboda ƙaunatattun'ya'yanku.Ku yi wa kanku ƙwaƙwal kamarungulu,Gama 'ya'yanku za su tafi bautartalala.