Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
12 verses
1Ni kuwa na ce, “Ku ji, ya kushugabannin mutanen Yakubu,Da ku sarakunan Isra'ila.Ya kamata ku san shari'a.
2Amma kuna ƙin nagarta, kunaƙaunar mugunta,Kuna feɗe mutanena,Kuna kuma fizge naman jikinsu dagaƙasusuwansu.
3Kuna cin naman mutanena, kunafeɗe fatar jikinsu,Kuna kakkarya ƙasusuwansu,Kuna yanyanka su gunduwagunduwa kamar naman da za a saa tukunya.”
4Sa'an nan za su yi kuka ga Ubangiji,Amma Ubangiji ba zai amsa musuba.Zai ɓoye musu fuskarsa a wannanlokaci,Saboda mugayen ayyukansu.
5Ga abin da Ubangiji ya ce a kanannabawan da suka bi damutanensa a karkace,Waɗanda suke cewa, “Salama,”sa'ad da suke da abinci,Amma sukan kai yaƙin shahadaGa wanda bai ba su abin sawa a bakaba.
6Saboda haka kome zai zama dareda duhu, ba wahayi ko duba.Rana za ta fāɗi a kan annabawa,Yini zai zama musu duhu baƙiƙirin.
7Masu gani za su sha kunya,Masu duba kuwa za su ruɗe,Dukansu za su rufe bakinsu,Gama ba amsa daga wurin Allah.
8Amma ni ina cike da iko,Da Ruhun Ubangiji,Da shari'a da ƙarfin hali,Don in sanar wa Yakubu da laifinsa,Isra'ila kuma da zunubinsa.
9Ku ji wannan, ya ku shugabanninjama'ar Yakubu,Da ku sarakunan mutanen Isra'ila,Ku da kuke ƙyamar shari'ar gaskiya,Kuna karkatar da dukan gaskiya.
10Kuna gina Sihiyona da jini,Kuna kuwa gina Urushalima dazalunci.
11Shari'ar shugabannin ƙasar ta cinhanci ce.Firistocinta suna koyarwa donneman riba,Haka kuma annabawa suna annabcidon neman kuɗi.Duk da haka suna dogara gaUbangiji, suna cewa,“Ai, Ubangiji yana tsakiyarmu,Ba masifar da za ta same mu.”
12Saboda ku kuwa za a nome Sihiyonakamar gona,Urushalima kuwa za ta zama tsibinkufai,Dutse inda Haikali yake zai zamakurmi.