Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
47 verses
1Firistoci da Lawiyawa da suka komo tare da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa, su neSeraiya, da Irmiya, da Ezra,
22-7 Amariya, da Malluki, da Hattush,Shekaniya, da Rehum, da Meremot,Iddo, da Ginneton, da Abaija,Miyamin, da Mawadiya, da Bilga,Shemaiya, da Yoyarib, da Yedaiya,Sallai, da Amok, da Halkiya, da Yedaiya.Waɗannan su ne shugabannin firistoci da 'yan'uwansu a zamanin Yeshuwa.
3[...]
4[...]
5[...]
6[...]
7[...]
88-9 Lawiyawa su ne,Yeshuwa, da Binnuyi, da Kadmiyel,Sherebiya, da Yahuza, da Mattaniya wanda yake lura da waƙoƙin godiya, da shi da 'yan'uwansa.Bukbukiya da Unno, 'yan'uwansu, suka tsaya daura da su a taron sujada.
9[...]
10Yeshuwa shi ne ya haifi Yoyakim, Yoyakim ya haifi Eliyashib, Eliyashib ya haifi Yoyada.
11Yoyada ya haifi Jonatan, Jonatan ya haifi Yadduwa.
1212-21 A zamanin Yoyakim babban firist, waɗannan su ne shugabannin iyalin firistoci,na wajen Seraiya, Meraiya nena wajen Irmiya, Hananiya nena wajen Ezra, Meshullam nena wajen Amariya, Yehohanan nena wajen Malluki, Jonatan nena wajen Shebaniya, Yusufu nena wajen Harim, Adana nena wajen Merayot, Helkai nena wajen Iddo, Zakariya nena wajen Ginneton, Meshullam nena wajen Abaija, Zikri nena wajen Miniyamin da Mowadiya, Filtai nena wajen Bilga, Shimeya nena wajen Shemaiya, Yehonatan nena wajen Yoyarib, Mattenai nena wajen Yedaiya, Uzzi nena wajen Sallai, Kallai nena wajen Amok, Eber nena wajen Hilkiya, Hashabiya nena wajen Yedaiya, Netanel ne.
13[...]
14[...]
15[...]
16[...]
17[...]
18[...]
19[...]
20[...]
21[...]
22A zamanin Eliyashib, da Yoyada, da Yohenan, da Yadduwa, Lawiyawa, har zuwa zamanin mulkin Dariyus, mutumin Farisa, aka rubuta shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa da firistoci.
23Aka kuma rubuta shugabannin gidajen kakannin zuriyar Lawi a tarihi, har zuwa zamanin Yohenan ɗan Eliyashib.
24Shugabannin Lawiyawa kuwa, su ne Hashabiya, da Sherebiya, da Yeshuwa, da Kadmiyel. 'Yan'uwansu suna tsaye kusa da su daki daki domin su yi yabo, su yi godiya kamar yadda Dawuda mutumin Allah ya umarta.
25Mattaniya, da Bakbukiya, da Obadiya, da Meshullam, da Talmon, da Akkub su ne masu tsaron ƙofofi, suna tsaron ɗakunan ajiya na wajen ƙofofi.
26Waɗannan suna nan a zamanin Yoyakim ɗan Yeshuwa, jikan Yehozadak, da zamanin mai mulki Nehemiya, da Ezra, firist da magatakarda.
27A lokacin keɓe garun Urushalima, sai aka nemo Lawiyawa a wurarensu duka don a kawo su Urushalima, su yi bikin keɓewa da farin ciki da godiya, da raira waƙoƙi da kuge, da garaya, da molo.
28Aka tattara mawaƙa daga kewayen Urushalima da ƙauyukan Netofatiyawa.
29Da kuma daga Betgilgal da karkarar Geba, da Azmawet, gama mawaƙan sun gina wa kansu ƙauyuka kewaye da Urushalima.
30Sai firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka kuma tsarkake jama'a, da ƙofofi, da garun.
31Sai na sa shugabannin Yahuza su hawo garu, sa'an nan na sa manyan ƙungiyoyi biyu waɗanda za su yi godiya, su tafi a jere.Ƙungiya guda ta bi wajen dama a kan garun zuwa Ƙofar Juji.
32Hoshaiya da rabin sugabannin Yahuza suka bi bayansu,
33tare da Azariya, da Ezra, da Meshullam,
34da Yahuza, da Biliyaminu, da Shemaiya, da Irmiya.
35Sa'an nan waɗansu 'ya'yan firistoci, masu busar ƙaho, su ne Zakariya ɗan Jonatan, jīkan Shemaiya. Sauran kakanninsa su ne Mattaniya, da Mikaiya, da Zakkur, daga zuriyar Asaf.
36Sauran 'yan'uwansa su ne Shemaiya, da Azarel, da Milalai, da Gilalai, da Ma'ai, da Netanel, da Yahuza, da Hanani. Suna da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗekaɗe. Ezra magatakarda ne yake gabansu.
37A Ƙofar Maɓuɓɓuga kuwa, sai suka yi gaba sosai wajen matakan birnin Dawuda, wajen hawan garu, daga bisa gidan Dawuda, zuwa Ƙofar Ruwa wajen gabas.
38Ƙungiyar jama'a ta biyu ta masu yin waƙoƙin godiya, ta bi ta wajen hagu. Na bi su tare da rabin jama'a a kan garu, sama da Hasumiyar Tanderu zuwa garu mai fādi,
39da Kuma sama da Ƙofar, Ifraimu da wajen Tsohuwar Ƙofar, da wajen Ƙofar Kifi, da Hasumiyar Hananel, da Hasumiyar Ɗari zuwa Ƙofar Tumaki, sai suka tsaya a Ƙofar Tsaro.
40Haka fa ƙungiyoyi biyu ɗin nan masu raira waƙoƙin godiya suka tsaya a Haikalin Allah.Ni da rabin shugabanni muna tare da su.
41Tare da firistoci kuma, wato su Eliyakim, da Ma'aseya, da Miniyamin, da Mikaiya, da Eliyehoyenai, da Zakariya, da Hananiya, suna busa ƙaho,
42da kuma Ma'aseya, da Shemaiya, da Ele'azara, da Uzzi, da Yehohanan, da Malkiya, da Elam, da Ezer, suna raira waƙoƙi, Yezrahiya kuma shi ne shugabansu.
43Jama'a suka miƙa hadayu da yawa a wannan rana, suka yi murna, gama Allah ya faranta musu zuciya ƙwarai. Mata da yara kuma suka yi murna. Aka ji muryar murnar mutanen Urushalima daga nesa.
44A ran nan aka sa mutanen da za su lura da ɗakunan ajiya, da sadakoki, da nunan fari, da zaka. Su ne za su tara nunan fari daga gonakin da suke kusa da garuruwa, bisa ga yadda doka ta ce, saboda firistoci da Lawiyawa, gama mutanen Yahuza sun yi murna saboda hidimar da firistoci da Lawiyawa suka yi.
45Sun yi wa Allahnsu sujada, sun yi hidimar tsarkakewa tare da mawaƙa da masu tsaron ƙofofi kamar yadda Dawuda da ɗansa Sulemanu suka umarta.
46A dā a zamanin Dawuda da Asaf akwai shugaban mawaƙa, akwai kuma waƙoƙin yabo da na godiya ga Allah.
47A zamanin Zarubabel da zamanin Nehemiya dukan jama'ar Isra'ila suka biya wa mawaƙa da masu tsaron ƙofofi bukatarsu ta kowace rana. Sun kuma ba Lawiyawa sadokoki, su Lawiyawa kuma suka ba zuriyar Haruna nasu rabo.