Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
21 verses
1Annabcin Obadiya ke nan.Wannan shi ne abin da Ubangiji Allah ya ce a kan al'ummar Edom.Ubangiji ya aiki manzonsa wurinsauran al'umma,Mun kuwa ji saƙonsa cewa,“Ku zo! Mu tafi mu yi yaƙi daEdom!”
2Ubangiji ya ce wa al'ummar Edom,“Zan maishe ki ƙanƙanuwa a cikinsauran al'umma,Za a raina ki ƙwarai.
3Girmankanki ya yaudare ki,Kina zaune a kagara, a kan dutse,Wurin zamanki yana canƙwanƙolin duwatsu.Don haka a zuciya kike cewa,‘Wa zai saukar da ni ƙasa?’
4Ko da yake kina shawagi can samakamar gaggafa,Gidanki kuma yana can cikin taurari,Daga can zan saukar da ke,” in jiUbangiji.
5“Idan ɓarayi sun shiga gidanki,Idan kuma 'yan fashi sun shigagidanki da dare,Yaya za su washe ki?Za su sace abin da ya ishe su nekaɗai,Idan kuma ɓarayin 'ya'yan inabisun shiga gonar inabinki,Za su bar miki kala kurum.
6Isuwa, wato Edom, ga taskarka,An washe ta ƙaƙaf!
7Waɗanda kake amana da su,Za su kore ka daga ƙasarka.Mutanen da suke amana da kai,Za su yaudare ka,Su ci ka da yaƙi.Abokan nan naka da kake ci tare dasu za su kafa maka tarko,Sa'an nan su ce, ‘Ina dukan wayonnan nasa?’ ”
8Ni Ubangiji na ce, “A ranar da zanhukunta Edom,Zan hallaka masu hikimarka,Zan shafe hikima daga dutsenIsuwa.
9Jarumawanka za su firgita, yaTeman,Za a kashe kowane mutum dagadutsen Isuwa.
10“Saboda kama-karyar da ka yi waYakubu ɗan'uwanka,Za a sa ka ka sha kunya,Za a hallaka ka har abada.
11A ranan nan ka tsaya kawai,A ranar da abokan gāba suka fasaƙofofinsa.Suka kwashe dukiyarsa,Suka jefa kuri'a a kan Urushalima.Ka zama kamar ɗaya daga cikinsu.
12Ba daidai ba ne ka yi murnaSaboda wahalar da ta samiɗan'uwanka.Ba daidai ba ne ka yi farin cikiSaboda halakar mutanen Yahuza.Ba daidai ba ne ka yi musu dariyaA ranar wahalarsu.
13Ba daidai ba ne ka shiga ƙofarjama'ataA ranar da suke shan masifa.Ba daidai ba ne ka yi murnaA kan bala'in ɗan'uwanka.Ba daidai ba ne ka washe dukiyarsaA ranar masifarsa.
14Ba daidai ba ne ka tsaya a mararraba,Don ka kashe waɗanda suke ƙoƙarintserewa.Ba daidai ba ne ka ba da waɗandasuka tsere a hannun maƙiyansuA ranar wahala.”
15“Ranar da ni Ubangiji zanshara'anta al'ummai duka ta zokusa,Ke, Edom, abin da kika yi,Shi ne za a yi miki.Ayyukanki za su koma a kanki.
16Kamar yadda kuka sha hukunci akan tsattsarkan dutsena,Haka dukan sauran al'umma za su yita sha.Za su sha, su yi tangaɗi,Su zama kamar ba su taɓa kasancewaba.”
17“Amma za a sami waɗanda za sutsira daga Dutsen Sihiyona,Dutsen zai zama wuri ne mai tsarki.Jama'ar Yakubu za ta mallakimallakarta.
18Jama'ar Yakubu za ta zama kamarwuta,Jama'ar Yusufu kuwa kamarharshen wuta,Jama'ar Isuwa za ta zama kamartattaka.Za su ƙone ta, su ci ta, ba wanda zaitsira.Ni Ubangiji na faɗa.”
19Isra'ilawan da yake Negeb za sumallaki dutsen Isuwa,Waɗanda suke a filaye na Yahuza za sumallaki ƙasar Filistiya.Isra'ilawa za su mallaki yankinƙasar Ifraimu da Samariya,Jama'ar Biliyaminu za su mallakiGileyad.
20Rundunar masu zaman talala naIsra'ilawaZa su mallaki Kan'aniyawa har zuwaZarefat.Masu zaman talala na Urushalima dasuke a SefaradZa su mallaki biranen Negeb.
21Isra'ilawa za su hau DutsenSihiyona, su cece shi,Za su mallaki dutsen Isuwa,Ubangiji ne Sarki.