Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
5 verses
1Bari dukan duniya ta raira waƙar farin ciki ga Ubangiji!
2Ku yi wa Ubangiji sujada da murna,Ku zo gabansa, kuna raira waƙoƙin farin ciki!
3Kada fa a manta da cewa, Ubangiji shi ne Allah!Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne,Mu jama'arsa ne, mu garkensa ne.
4Ku shiga Haikalinsa da godiya,Ku shiga wurinsa mai tsarki, ku yabe shi!Ku gode masa, ku yabe shi!
5Ubangiji nagari ne,Ƙaunarsa madawwamiya ce,Amincinsa kuwa har abada abadin ne.