Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
7 verses
1Na dogara ga Ubangiji domin zaman lafiya,Wauta ce idan kun ce mini,“Ka yi firiya kamar tsuntsu zuwa duwatsu,
2Domin mugaye sun ja bakkunansu,Sun kuma ɗana kibansuDomin su harbi mutanen kirki a duhu.
3Ba abin da mutumin kirki zai iya yiSa'ad da kome ya lalace.”
4Ubangiji yana cikin tsattsarkan Haikalinsa,Yana da kursiyinsa a Sama.Yana kallon dukan mutaneYana sane da abin da suke yi.
5Yana auna masu kirki da mugaye dukka,Yana ƙin marar bin doka gaba ɗaya.
6Yakan aukar da garwashin wutaDa kibritu mai cin wuta a kan mugaye,Yakan hukunta su da harshen wuta mai ƙuna.
7Ubangiji mai adalci ne, yana ƙaunar kyawawan ayyuka,Masu yi masa biyayya za su zauna a gabansa.