Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
9 verses
1Yabo Ya tabbata ga Ubangiji!Ku bayin Ubangiji,Ku yabi sunansa!
2Za a yabi sunansa yanzu da har abada!
3Daga gabas zuwa yamma a yabi sunan Ubangiji!
4Ubangiji yake mulkin dukan sauran al'umma,Ɗaukakarsa tana bisa kan sammai.
5Ba wani kamar Ubangiji Allahnmu.Yana zaune a can ƙwanƙolin sama,
6Amma ya duba ƙasa,Ya dubi sammai da duniya.
7Yakan ɗaga talakawa daga ƙura,Yakan ɗaga matalauta daga cikin azabarsu.
8Yakan sa su zama abokan sarakuna,Sarakunan jama'arsa.
9Yakan girmama matar da ba ta haihuwa a gidanta,Yakan sa ta yi farin ciki ta wurin ba ta 'ya'ya.Yabo ya tabbata ga Ubangiji!