Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
19 verses
1Ina ƙaunar Ubangiji, saboda yana jina,Yana kasa kunne ga addu'o'ina.
2Yakan kasa kunne gare ni,A duk lokacin da na yi kira gare shi.
3Mutuwa ta ɗaure ni da igiyarta tam,Razanar kabari ta auka mini,Na cika da tsoro da alhini.
4Sa'an nan sai na yi kira ga Ubangiji, na ce,“Ina roƙonka, ya Ubangiji, ka cece ni!”
5Ubangiji mai jinƙai ne, mai alheri,Allahnmu mai rahama ne.
6Ubangiji yakan kiyaye kāsassu,Sa'ad da na shiga hatsari ya cece ni.
7Kada ki yi shakka, ya zuciyata,Gama Ubangiji yana yi mini alheri.
8Ubangiji ya cece ni daga mutuwa,Ya share hawayena,Bai bari a kāshe ni ba.
9Don haka nake tafiya a gaban UbangijiA duniyar masu rai.
10Na dai yi ta gaskatawa, ko da yakeNa ce, “An ragargaza ni sarai.”
11Sa'ad da na ji tsoro na ce,“Ba wanda za a iya dogara gare shi.”
12Me zan bayar ga UbangijiSaboda dukan alheransa gare ni?
13Zan miƙa hadaya ta sha ga Ubangiji,Ina gode masa domin dā ya cece ni.
14Zan ba shi abin da na alkawartaA taron dukan jama'arsa.
15Mutuwar ɗaya daga cikin tsarkakansa,Abu mai daraja ne!
16Ni bawanka ne, ya Ubangiji,Ina bauta maka yadda mahaifiyata ta yi,Ka 'yantar da ni.
17Zan miƙa maka hadaya ta godiya,Zan yi addu'ata a gare ka.
18A taron dukan jama'arka,A shirayun Haikalinka,A Urushalima, zan ba ka abin da na alkawarta.Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
19[...]