Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
7 verses
1Sa'ad da nake shan wahala,Na yi kira ga Ubangiji,Ya kuwa amsa mini.
2Ka cece ni, ya Ubangiji,Daga maƙaryata da masu ruɗi!
3Ku maƙaryata, me Allah zai yi da ku?Yaya zai hukunta ku?
4Da kibau masu tsini na mayaƙa,Da garwashin wuta zai hukunta ku!
5Zama tare da ku mugun abu ne, kamar zama a Meshek,Ko tare da mutanen Kedar!
6Na daɗe ƙwarai ina zama tare da mutane marasa son salama!
7Sa'ad da nake maganar salama,Su sai su yi ta yaƙi.