Hausa Holy Bible Wordproject Bible
3 verses
1'Ya Ubangiji, na rabu da girmankai,Na bar yin fariya,Ba ruwana da manyan al'amura,Ba ruwana kuma da zantuttukan da suka fi ƙarfina.
2Amma na haƙura, raina a kwance,Kamar jinjirin da yake kwance jalisan a hannun mahaifiyarsa,Haka zuciyata take kwance.
3Ya Isra'ila, ka dogara ga Ubangiji,Daga yanzu har abada!