Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
6 verses
1Yabo ya tabbata ga Ubangiji!Ku yabi Allah a cikin Haikalinsa!Ku yabi ƙarfinsa a sama!
2Ku yabe shi saboda manyan abubuwaWaɗanda ya aikata!Ku yabi mafificin girmansa!
3Ku yabe shi da kakaki!Ku yabe shi da garayu da molaye!
4Ku yabe shi da bandiri kuna taka rawa!Ku yabe shi da garayu da sarewa!
5Ku yabe shi da kuge!Ku yabe shi da kuge masu amo!
6Ku yabi Ubangiji dukanku rayayyun talikai.Yabo ya tabbata ga Ubangiji!