Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
9 verses
1Ubangiji ya amsa maka a ranar wahala!Allah na Yakubu ya kiyaye ka!
2Ya aiko maka da taimako daga Haikalinsa,Ya kawo maka gudunmawa daga Sihiyona.
3Ya karɓi hadayunka,Ya kuma ji daɗin dukan sadakokinka.
4Ya ba ka abin da kake bukata,Ya sa dukan shirye-shiryenka su yi nasara.
5Mu kuma, sai mu yi sowa ta farin ciki saboda ka ci nasara,Mu yi bikin cin nasara da ka yi,Da yabon Ubangiji Allahnmu.Allah ya amsa dukan roƙe-roƙenka!
6Yanzu dai na sani Ubangiji yakan ba da nasara ga zaɓaɓɓen sarkinsa,Yakan amsa masa daga samaniyarsa mai tsarki,Da ikonsa mai girma yakan sa shi yă yi nasara.
7Waɗansu ga karusan yaƙinsu suke dogara,Waɗansu kuwa ga dawakansu,Amma mu, ga ikon Ubangiji Allahnmu muke dogara!
8Za su yi tuntuɓe su fāɗi,Amma mu za mu tashi mu tsaya daram!
9Ka ba sarki nasara, ya Ubangiji,Ubangiji zai amsa mana sa'ad da muka yi kira.