Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
12 verses
1Ka hurta rashin laifina, ya Ubangiji,Gama na yi abin da suke daidai,Na dogara gare ka gaba ɗaya.
2Ka jarraba ni ka auna ni, ya Ubangiji,Ka gwada muradina da tunanina.
3Madawwamiyar ƙaunarka tana bi da ni,Amincinka yake yi mini jagora kullayaumin.
4Ba na tarayya da mutanen banza,Ba abin da ya gama ni da masu riya.
5Ina ƙin tarayya da masu mugunta,Nakan kauce wa mugaye.
6Ya Ubangiji, na wanke hannuwanaDon in nuna ba ni da laifi,Da ibada nakan taka, ina kewaya bagadenka.
7Na raira waƙar godiya,Na faɗi dukan ayyukanka masu banmamaki.
8Ya Ubangiji, ina ƙaunar Haikali inda zatinka yake,Inda ɗaukakarka yake zaune.
9Kada ka hallaka ni tare da masu zunubi,Ka cece ni daga ƙaddarar masu kisankai,
10Mutanen da suke aikata mugunta a dukan lokaci,A koyaushe suna shirye don su ba da rashawa.
11Amma ni, ina yin abin da yake daidai,Ka yi mini jinƙai ka fanshe ni!
12Na kuɓuta daga dukan hatsarori,A taron sujada na yabi Ubangiji!