Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
13 verses
1Mai farin ciki ne wanda yake kula da matalauta,Ubangiji zai taimake shi sa'ad da yake shan wahala.
2Ubangiji zai kiyaye shi, yă keɓe ransa.Ubangiji zai sa yă ji daɗi a ƙasar,Ba zai bar shi a hannun magabtansa ba.
3Ubangiji zai taimake shi sa'ad da yake ciwoYa mayar masa da lafiyarsa.
4Na ce, “Na yi maka zunubi, ya Ubangiji,Ka yi mini jinƙai ka warkar da ni!”
5Magabtana suna mugayen maganganu a kaina,Suna cewa, “Yaushe ne zai mutu a manta da shi?”
6Masu zuwa su gaishe ni ba da zuciya ɗaya suke zuwa ba,Sukan tattara duk mugun labari a kainaSa'an nan su je su yi ta bazawa ko'ina.
7Maƙiyana duk suna raɗa da junansu a kaina,Sukan ɗauka na fi kowa mugunta.
8Suna cewa, “Yana ciwon ajali,Ba zai taɓa tashi daga gadonsa ba.”
9Har da shaƙiƙin abokina,Wanda na fi amincewa da shi.Wanda muke ci tare, ya juya yana gāba da ni.
10Ka ji ƙaina ya Ubangiji, ka maido mini da lafiyata,Zan kuwa sāka wa magabtana!
11Zan sani kana jin daɗina,Domin ba za su rinjaye ni ba,
12Za ka taimake ni domin ina yin abin da yake daidai,Za ka sa ni a gabanka har abada.
13Bari mu yabi Ubangiji, Allah na Isra'ila.Ku yabe shi yanzu da har abada!Amin! Amin!