Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
5 verses
1Ya Allah, ka kuɓutar da ni,Ka kiyaye al'amarina daga marasa tsoronka,Ka cece ni daga ƙaryar mugaye!
2Ya Allah, kai ne kake kāre ni,Me ya sa ka yashe ni?Me ya sa nake ta shan wahala saboda muguntar maƙiyana?
3Ka aiko da haskenka, da gaskiyarka,Bari su bishe ni,Su kawo ni Sihiyona, tsattsarkan tudunka,Su kawo ni Haikalinka, inda zatinka yake!
4Sa'an nan zan tafi wurin bagadenka, ya Allah,Zuwa gare ka, kai wanda kake sa ni in yi murna da farin ciki,In raira waƙar yabo a gare ka da garayata,Ya Allah, Allahna!
5Me ya sa nake baƙin ciki?Me ya sa nake damuwa?Zan dogara ga Allah,Zan ƙara yabonsa,Mai Cetona, Allahna.