Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
7 verses
1Ka cece ni ta wurin ikonka, ya Allah,Ka cece ni ta wurin ƙarfinka!
2Ka ji addu'ata, ya Allah,Ka saurari kalmomina!
3Masu girmankai sun tasar mini,Mugaye suna nema su kashe ni,Mutanen da ba su kula da Allah ba.
4Na sani Allah ne mai taimakona,Na sani Ubangiji shi ne mai tsarona!
5Ubangiji ya hukunta wa maƙiyana da irin muguntarsu!Gama zai hallaka su saboda shi mai aminci ne.
6Da murna zan miƙa maka hadaya,Zan yi maka godiya, ya Ubangiji,Domin kai mai alheri ne.
7Ka cece ni daga dukan wahalaina,Na kuwa ga an kori maƙiyana.