Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
10 verses
1Ya Ubangiji, kada ka yi fushi, ka kuma tsauta mini!Kada ka hukunta ni da fushinka!
2Ka ji tausayina, gama na gaji tiƙis,Ka wartsarkar da ni, gama na tafke sarai.
3Duk na damu ƙwarai da gaske.Sai yaushe wannan zai ƙare, ya Ubangiji?
4Ya Ubangiji, ka zo ka cece ni,Gama kana ƙaunata, ka kuɓutar da ni daga mutuwa.
5Ba za a tuna da kai a lahira ba,Ba wanda zai yabe ka a can!
6Na gaji tiƙis saboda baƙin ciki,Kowane dare gadona yakan jiƙe saboda kukana.Matashin kaina ya yi sharkaf da hawaye.
7Idanuna sun yi kumburi saboda yawan kuka,Har da ƙyar nake iya gani,Duk kuwa saboda abokan gābana!
8Ku tafi daga nan, ku masu aikin mugunta!Ubangiji yana jin kukana.
9Yana kasa kunne ga kukana na neman taimako,Yana kuwa amsa addu'o'ina.
10Abokan gābana duka za su sha kunyar fāɗuwarsu,Suna cikin matsanancin ruɗami,Za a kwashe su farat ɗaya.