Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
8 verses
1Ya Allah, ka ji kukana,Ka ji addu'ata!
2Sa'ad da nake nesa da gida, zuciyata ta karai,Zan yi kira gare ka!Ka kai ni lafiyayyiyar mafaka.
3Kai ne kāriyata mai ƙarfiDa take kiyaye ni daga maƙiyana.
4Ka yarda in zauna a alfarwarka dukan kwanakin raina,Ka yarda in sami zaman lafiya a ƙarƙashin fikafikanka.
5Ya Allah, kā ji alkawaraina,Kā kuwa ba ni abin da ya dace,Tare da waɗanda suke ɗaukaka ka.
6Ka ƙara wa sarki tsawon rai,Ka sa ya rayu dukan lokaci!
7Ka sa ya yi mulki har abada a gabanka, ya Allah,Ka tsare shi da madawwamiyar ƙaunarka, da amincinka.
8Don haka zan yi ta raira waƙar yabonka kullayaumin,A sa'ad da nake miƙa maka abin da na alkawarta.