Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
11 verses
1Ya Allah, kai ne Allahna,Ina sa zuciya gare ka.Duk niyyata ta nemanka ce,Raina yana ƙishinka,Kamar bussasshiyar ƙasa,Wadda ta zozaye, ba ta da ruwa.
2Bari in gan ka a tsattsarkan wurinka,In dubi ɗaukakarka da darajarka.
3Madawwamiyar ƙaunarka ta fi rai kansa,Saboda wannan zan yabe ka.
4Muddin raina, zan yi maka godiya,Zan ta da hannuwana sama, in yi addu'a gare ka.
5Raina zai yi liyafa, yă ƙoshi sosai,Ni kuwa zan raira waƙoƙin murna na yabo a gare ka.
6Sa'ad da nake kwance a gadona na tuna da kai,Dare farai ina ta tunawa da kai,
7Domin kai kake taimakona kullayaumin.Da murna, nake raira waƙa,A inuwar fikafikanka,
8Raina yana manne maka,Ikonka yana riƙe da ni.
9Waɗanda suke ƙoƙari su kashe ni,Za su gangara zuwa lahira,
10Za a kashe su cikin yaƙi,Kyarketai kuwa za su cinye gawawwakinsu.
11Sarki zai yi farin ciki ga Allah,Duk waɗanda suka yi alkawarai da sunan AllahZa su yi murna,Amma za a rufe bakunan maƙaryata.