Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
12 verses
1Allah sananne ne a Yahuza,Mashahuri ne kuma a Isra'ila.
2Wurin zamansa yana Urushalima,A dutsen Sihiyona zatinsa yake.
3A can yake kakkarya kiban abokan gāba,Da garkuwoyinsu, da takubansu, i, har da dukan makamansu.
4Ina misalin darajarka, ya Allah!Ina misalin ɗaukakarka a sa'ad da ka komo daga kan duwatsu,Daga korar abokan gābanka!
5An kwashe ganimar sojojinsu masu ƙarfin hali,Yanzu suna barci, barcin matattu,Ba waninsu da ya ragu,Da zai yi amfani da makamansa.
6Sa'ad da ka fafare su, ya Allah na Yakubu,Dawakansu da mahayansu suka fāɗi matattu.
7Amma mutane suna jin tsoronka!Wa zai iya tsayawa a gabankaSa'ad da ka yi fushi?
8Daga Sama ka sanar da shari'arka,Duniya ta tsorata, ta yi tsit,
9Sa'ad da ka tashi domin ka yanke hukunci,Domin ka ceci waɗanda ake zalunta a duniya.
10Hasalar mutane ba ta ƙara kome, sai dai ta ƙara maka yabo.Waɗanda suka tsira daga yaƙe-yaƙe za su kiyaye idodinka.
11Ku ba Ubangiji Allahnku abin da kuka alkawarta masa,Dukanku sauran al'umma da kuke kusa, ku kawo masa kyautai.Allah yakan sa mutane su ji tsoronsa,
12Yakan ƙasƙantar da shugabanni masu girmankai,Ya tsoratar da manyan sarakuna.