Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
9 verses
1Ya Ubangiji, Ubangijinmu,An san girmanka ko'ina a dukan duniya.Yabonka ya kai har sammai,
2Yara da jarirai suna raira shi,Ka gina kagara saboda magabtanka,Domin ka tsai da maƙiyanka da abokan gābanka.
3Sa'ad da na duba sararin sama, wanda ka yi,Da wata da taurari waɗanda ka sa a wuraren zamansu,
4Wane ne mutum, har da kake tunawa da shi,Mutum kurum, har da kake lura da shi?
5Duk da haka in banda kai ba wanda ya fi shi,Ka naɗa shi da daraja da girma!
6Ka sa shi ya yi mulkin dukan abin da ka halitta,Ka ɗora shi a kan dukan abubuwa,
7Tumaki da shanu, har ma da namomin jeji,
8Da tsuntsaye da kifaye,Da dukan halittar da suke cikin tekuna.
9Ya Ubangiji, Ubangijinmu,An san girmanka ko'ina a dukan duniya!