Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
13 verses
1Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji!Ku raira waƙa ga Ubangiji, ya duniya duka!
2Ku raira waƙa ga Ubangiji, ku yabe shi!Kowace rana ku ba da labari mai daɗi cewa,“Ya cece mu!”
3Ku yi shelar ɗaukakar Ubangiji ga sauran al'umma,Ku yi shelar ayyukansa masu girma ga dukan kabilai.
4Ubangiji da girma yake, tilas a ɗaukaka shi,Tilas a fi jin tsoronsa fiye da dukan alloli.
5Allolin dukan al'ummai, gumaka ne kawai,Amma Ubangiji ne ya yi sammai.
6Daraja da ɗaukaka suna kewaye da shi,Girma da jamali suna cikin Haikalinsa.
7Dukan jama'ar da suke bisa duniya su yabi Ubangiji!Ku yabi ɗaukakarsa da ikonsa!
8Ku yabi sunan Ubangiji mai ɗaukaka,Ku kawo sadaka, ku shiga Haikalinsa.
9Ku durƙusa a gaban Mai Tsarki, sa'ad da ya bayyana,Ku yi rawar jiki a gabansa, ku duniya duka!
10A faɗa wa dukan sauran al'umma, “Ubangiji Sarki ne!Duniya ta kahu da ƙarfi a wurin zamanta,Ba za a iya kaushe ta ba,Shi zai shara'anta dukan jama'a da adalci.”
11Duniya da sararin sama, ku yi murna!Ki yi ruri, ya ke teku da dukan masu rai da suke cikinki,
12Ku yi murna ya ku filaye da dukan abubuwan da suke cikinku!Sa'an nan itatuwan da suke cikin kuramaZa su ta da murya saboda farin ciki
13A gaban Ubangiji, gama ya zo ne ya mallaki duniya.Zai mallaki dukan jama'ar duniyaDa adalci da gaskiya.