Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
17 verses
1To, ina gani sa'ad da Ɗan Ragon nan ya ɓamɓare ɗaya daga cikin hatiman nan bakwai, na ji ɗaya daga cikin rayayyun halittan nan huɗu ta yi magana kamar aradu ta ce, “Zo.”
2Da na duba, ga farin doki, mahayinsa kuma yana da baka, aka ba shi kambi, ya kuwa fita yana mai nasara, domin ya ƙara cin nasara.
3Da ya ɓamɓare hatimi na biyu, na ji rayayyiyar halittar nan ta biyu ta ce, “Zo.”
4Sai wani jan doki ya fito, aka kuma ba mahayinsa izini yă ɗauke salama daga duniya, don mutane su kashe juna, aka kuma ba shi babban takobi.
5Da ya ɓamɓare hatimi na uku, na ji rayayyiyar halittar nan ta uku ta ce, “Zo.” Da na duba, ga baƙin doki, mahayinsa kuwa da mizani a hannunsa.
6Sai na ji kamar wata murya a tsakiyar rayayyun halittar nan huɗu tana cewa, “Mudun alkama dinari guda, mudu uku na sha'ir dinari guda, sai dai kada ka ɓāta mai da kuma ruwan inabi!”
7Da ya ɓamɓare hatimi na huɗu, na ji muryar rayayyiyar halittan nan ta huɗu ta ce, “Zo.”
8Da na duba, ga doki kili, sunan mahayinsa kuwa Mutuwa, Hades kuma tana biye da shi. Sai aka ba su iko a kan rubu'in duniya, su yi kisa da takobi, da yunwa, da annoba, da kuma namomin jeji na duniya.
9Da ya ɓamɓare hatimi na biyar, na ga rayukan waɗanda aka kashe saboda Maganar Allah, da shaidar da suka yi a ƙarƙashin bagadin ƙona turare.
10Sai suka ta da murya da ƙarfi suka ce, “Ya Ubangiji Mamallaki, Mai Tsarki, Mai Gaskiya, sai yaushe ne za ka yi hukunci, ka ɗaukar mana fansar jininmu a gun mazaunan duniya?”
11Sai aka ba kowannensu farar riga, aka ce musu, su dai huta kaɗan, har a cika adadin abokan bautarsu, wato, 'yan'uwansu, waɗanda za a kashe, kamar yadda su ma aka kashe su.
12Da ya ɓamɓare hatimi na shida, na duba, sai kuwa aka yi wata babbar rawar ƙasa, rana ta koma baƙa kamar gwado na gashi, gudan wata ya zama kamar jini,
13taurari kuma suka faɗa a ƙasa kamar yadda ɓaure yake zubar da ɗanyun 'ya'yansa, in ƙasaitacciyar iska ta kaɗa shi,
14sararin sama ya dāre ya naɗe kamar tabarma, sai aka kawar da kowane dutse, da kowane tsibiri daga mazauninsa.
15Sai sarakunan duniya, da manyan mutane, da sarakunan yaƙi, da ma'arzuta, da ƙarfafa, da kuma kowane bawa da ɗa, suka ɓuya a kogwanni, da kuma a cikin duwatsu,
16suna ce wa duwatsun, “Ku faɗo a kanmu, ku ɓoye mu daga idon wanda yake a zaune a kan kursiyin, da kuma fushin Ɗan Ragon nan,
17don babbar ranar fushinsu ta zo, wa kuwa zai iya jure mata?”