Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
14 verses
1Taku ta ƙare, ku da kuke zamansakewa a Sihiyona,Da ku da kuke tsammani kunazaman lafiya a Samariya,Ku da kuke manyan mutaneNa wannan babbar al'umma taIsra'ila,Waɗanda jama'a suke zuwa a gare suneman taimako!
2Ku je ku duba a birnin Kalne.Sa'an nan ku zarce zuwa babbanbirnin Hamat,Har zuwa birnin Gat ta Filistiyawa.Sun fi mulkin Yahuza da Isra'ila ne?Ko kuwa, yankin ƙasarsu ya finaku?
3Kuna ƙoƙari ku kauce wa wannanrana ta masifa,Amma ga shi, goyon bayan hargitsikuke ta yi,Ta wurin ayyukanku.
4Taku ta ƙare, ku da kuke kwancekan gadajen hauren giwa,Kuna jin daɗin miƙe jiki a dogayenkujerunku,Ku ci naman maraƙi da na rago.
5Kukan so ku tsara waƙoƙi kamaryadda Dawuda ya yi,Ku raira su da garayu.
6Da manyan kwanoni kuke shanruwan inabi,Ku shafe jiki da mai mafi kyau,Amma ba ku yin makoki sabodalalacewar Isra'ila.
7Don haka, ku ne na fari da za a sa suyi ƙauraBukukuwanku da shagulgulanku zasu ƙare.
8Ubangiji kansa ne ya rantse.Ubangiji Allah Mai Runduna ya ce,“Ba na son girmankai na jama'arIsra'ila.Ba na son fādodinsu.Zan ba da birnin da dukan abin dayake cikinsa ga abokan gābansu.”
9Ko da a ce mutum goma ne suka ragu a gida guda, duk za su mutu.
10Sa'ad da dangin mamacin ya shiga don ya fitar da gawar, ya ƙone, sai ya yi kira ga ko wane ne da yake ɓoye a gidan, ya ce, “Ko akwai wani kuma a nan?”Sai a amsa, “A'a.”Zai ce, “Kul! Kada a ambaci sunan Ubangiji.”
11Sa'ad da Ubangiji ya ba da umarni, babban gida da ƙarami rushewa za su yi.
12Dawakai sukan yi sukuwa aduwatsu?Ana huɗan teku da garmarshanu?Duk da haka kuka mai da adalcidafi,Kuka mai da nagarta, mugunta.
13Kuna fariyar cin garin Lodebar, watowofi, da yaƙi.Kun ce, “Ƙarfinmu ya isa har mu ciKarnayim, wato ƙaho biyu, dayaƙi.”
14Ubangiji Allah Mai Rundunakansa, ya amsa ya ce,“Zan aiko da wata al'umma ta yigāba da ku, ya Isra'ilawa.Za ta matse mukuTun daga mashigin Hamat wajenarewa,Har zuwa Kwarin Urdun a kudu.”