Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
27 verses
1Ku kasa kunne, ku jama'arIsra'ila, ga waƙar makoki da zan yia kanku.
2Isra'ila ta fāɗi,Ba kuwa za ta ƙara tashi ba.Tana fa kwance a ƙasa,Ba wanda zai tashe ta.
3Ubangiji ya ce,“Wani birnin Isra'ila ya aika da sojadubu,Ɗari ne kaɗai suka komo,Wani birni kuma ya aika da soja ɗarine,Amma goma kaɗai suka komo.”
4Ubangiji ya ce wa jama'ar Isra'ila,“Ku zo gare ni, za ku tsira.
5Kada ku tafi ku yi sujada a Biyer-sheba.Kada ku yi ƙoƙarin nemana aBetel,Gama Betel lalacewa za ta yi.Kada ku tafi Gilgal,Gama an ƙaddara wa jama'arta suyi ƙaura.”
6Ku tafi wurin Ubangiji ku tsira.Idan kuwa kun ƙi,Shi zai babbaka jama'ar YusufuKamar yadda a kan babbaka dawuta.Wuta za ta ƙone jama'ar Betel,Ba kuwa mai kashe wutar.
7Abin tausayi ne ku da kuke ɓatashari'a,Kuna hana wa mutane hakkinsu.
8Ubangiji ne ya yi taurarinKaza da 'ya'yantaDa mai farauta da kare.Ya mai da duhu haske,Rana kuwa dare.Shi ya kirawo ruwan teku yabayyana,Ya shimfiɗa shi a bisa ƙasa.Sunansa Ubangiji ne.
9Ya kawo halaka a kan ƙarfafa,Da a kan birane masu garu.
10Kun ƙi wanda ya tsaya a kanadalci,Da mai faɗar ainihin gaskiya a gabanshari'a.
11Kun matsa wa talakawa lamba,Kun ƙwace musu abincinsu.Saboda haka kyawawan gidajen nanda kun gina da dutse,Ba za ku zauna a cikinsu ba,Ba kuwa za ku sha ruwan inabinnanDaga kyawawan gonakin inabinkuba.
12Na san irin zunuban da kuke yi,Da mugayen laifofin da kuka aikata.Kuna wulakanta mutanen kirki,Kuna cin hanci,Kuna hana a yi wa talakawa shari'aradalci a majalisa.
13Ashe, ba abin mamaki ba ne,Da masu hankali suka kame bakinsuA waɗannan kwanaki na mugunta.
14Ku yi ƙoƙari, ku yi nagarta, bamugunta ba,Domin ku tsira.Sa'an nan ne Ubangiji AllahMaɗaukakiZai kasance tare da ku sosai,Kamar yadda kuka ɗauka!
15Ku ƙi mugunta, ku ƙaunacinagarta,Ku yi adalci cikin majalisaralƙalanku!Watakila Ubangiji Allah MaiRundunaZai yi wa sauran da suka ragu nawannan al'umma alheri.
16Haka Ubangiji Allah Mai Rundunaya ce,“Za a yi kuka, a yi kururuwa atitunan birninku saboda azaba.Daga ƙauyuka za a kirawomutaneSu zo su yi makokin.Waɗanda suka mutu, tare da masumakoki da aka ijarar da su.
17Za a yi kuka ko'ina cikin dukangonakin inabinkuGama zan zo in yi muku horo.”
18Taku ta ƙare, ku da kuke marmarinzuwan ranan nan ta Ubangiji!Wane amfani wannan rana za ta yimuku?Rana ta baƙin ciki ce,Ba ta murna ba.
19Zai zama kamar wanda ya tsere wazakiYa fāɗa a bakin beyar!Ko kuwa kamar wanda ya komogida,Ya dāfa bango, maciji ya sare shi.
20Ranar Ubangiji za ta kawo baƙinciki,Ba murna ba.Rana ce ta damuwa ba ta fara'a ba.
21Ubangiji ya ce,“Na ƙi bukukuwanku na addini.Ina ƙyamarsu!
22Sa'ad da kuka kawo mini hadayunƙonawaDa hadayunku na tsaba, ba zankarɓa ba.Ba kuma zan karɓi turkakkundabbobinkuWaɗanda kuka miƙa mini hadayungodiya ba.
23Ku yi shiru da yawan hargowarwaƙoƙinku.Ba na so in saurari kaɗe-kaɗenku dabushe-bushenku.
24Sai ku sa adalci da nagarta su gudanoa yalwaceKamar kogin da ba ya ƙafewa.
25“Ya ku, jama'ar Isra'ila, ai, a waɗannan shekaru arba'in da kuka yi cikin jeji kuka kawo mini sadaka da hadayu,
26duk da haka, kuka ɗauki siffofin gumakanku na taurari, wato Sakkut da Kaiwan, waɗanda kuka yi wa kanku.
27Ni kuwa zan sa ku yi ƙaura zuwa wata ƙasa gaba da Dimashƙu.” Ubangiji, Allah Mai Runduna, shi ne ya faɗa.