Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
13 verses
1Ku kasa kunne ga wannan, ya kumatan Samariya,Ku da kuka yi ƙiba kamarturkakkun shanu,Ku da kuke wulakanta kasassu,Kuna yi wa matalauta danniya,Kukan umarci mazajenku,Ku ce, “Kawo mini abin sha!”
2Da yake Ubangiji Mai Tsarki neYa riga ya yi alkawari,Ya ce, “Hakika kwanaki za su zoDa za a jawo ku da ƙugiyoyi,Kowannenku zai zama kamar kifi aƙugiya.
3Za a kwashe ku, a fitar da kuTa inda garu ya tsage na mafi kusaduka, a jefar.”
4Ubangiji ya ce,“Jama'ar Isra'ila,Ku tafi Betel, tsattsarkan wuri,Ku yi ta zunubi!Ku tafi Gilgal ku ƙara zunubi!Ku yi ta kawo dabbobi sadakakowace safiya.A kowace rana ta ukuKu yi ta ba da zaka.
5Ku miƙa abincinku hadaya tagodiya.Ku yi ta yin fariya da hadayarku tayardar rai!Gama irin abin da kuke jin daɗin yike nan.”
6Ubangiji ya ce,“Ai, ni ne, na sa a yi yunwa abiranenku.Shi ya sa ba ku da abinci.Duk da haka ba ku juyo gare ni ba.
7Na hana wa shuke-shukenku ruwaA lokacin da suka fi bukata.Na sa a yi ruwa a wani birni,A wani birni kuwa na hana,Wata gonar ta sami ruwan sama,Amma wadda ba ta samu ba tabushe.
8Ƙishirwa ta sa jama'a su tafke harbirane biyu ko ukuSuka tafi neman ruwa a birnin dasuke maƙwabtaka da shi,A nan ma ba su sami isasshen ruwansha ba,Duk da haka ba ku komo wurinaba.
9“Na sa darɓa, da domanaSu lalatar da amfanin gonakinku.Fāra kuma ta cinye lambunankuDa gonakin inabinku, da itatuwanɓaurenku,Da na zaitun ɗinku.Duk da haka ba ku komo wurina ba.
10“Na aukar muku da annoba irinwadda na aukar wa Masar.Na karkashe samarinku a wurinyaƙi,Na kwashe dawakanku.Na cika hancinku da ɗoyinsansaninku.Duk da haka ba ku komo wurina ba.
11“Na hallakar da waɗansunkuKamar yadda na hallakar da Sadumada Gwamrata.Kamar sanda kuke, wanda aka fizgedaga wuta.Duk da haka ba ku komo wurinaba.
12Saboda haka, jama'ar Isra'ila,Ga abin da zan yi muku,Zan kuwa yi shi duk,Sai ku yi shirin zuwa gabanUbangiji.”
13Allah ne ya yi duwatsuYa kuma halicci iska.Ya sanar da nufinsa ga mutum,Ya juya rana ta zama dare.Yana sarautar duniya duka.Sunansa kuwa Ubangiji Maɗaukaki!