Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
15 verses
1Jama'ar Isra'ila, ku kasa kunne ga wannan saƙo da Ubangiji ya aiko muku, ya ce, “Na fitar da iyalanku duka daga Masar.
2“Daga cikin dukan al'umman da nakeƙauna a duniya,Ku kaɗai ne na sani,Nake kuma kulawa da ku,Don haka zan hukunta ku sabodazunubanku.”
3Zai yiwu a ce mutum biyu za su yitafiya tare,Amma su rasa shirya magana?
4Zai yiwu zaki yă yi ruri a jejiBa tare da ya kama nama ba?Zai yiwu sagarin zaki yă yi gurnani akogonsaIn bai kama wani abu ba?
5Zai yiwu tsuntsu ya fāɗi ƙasaIn ba a kafa masa tarko ba?Zai yiwu tarko ya zarguIn bai kama wani abu ne ba?
6Zai yiwu mutane su rasa firgita,Idan aka busa ƙahon yaƙi abirni?Zai yiwu wata babbar masifa ta aukowa birniBa da yardar Ubangiji ba?
7Hakika Ubangiji ba yakan aikatakome ba,Sai da sanin bayinsa annabawa.
8Zaki ya yi ruri!Wa ba zai ji tsoro ba?Sa'ad da Ubangiji ya yi magana!Wa zai ƙi yin shelar maganarsa?
9Ka yi shela ga mazaunan fādar Ashdod da Masar, ka ce, “Duk ku taru a Samariya ku ga irin babban shashancin da ake yi a can, ku ga irin laifofin da ake aikatawa a birnin.”
10Ubangiji ya ce, “Waɗannan mutane suka cika gidajensu masu daraja da abubuwan da suka samo ta hanyar zamba, da ta kama-karya. Ta yadda za su yi su yi aminci ma, ba su sani ba.
11“Saboda haka abokan gaba za sukewaye ƙasarsu,Su hallakar da kagaransu,Su washe gidajen nan nasu masudaraja.”
12Ubangiji ya ce,“Kamar yadda makiyayi yakan ceciƙafafu biyuKo kunne ɗaya na tunkiya dagabakin zaki,Haka nan kuma kima daga cikinmutanen SamariyaWaɗanda suke zaman jin daɗi za sutsira.
13Ku saurara yanzu,Ku yi wa zuriyar Yakubu kashedi,”In ji Ubangiji, Maɗaukaki.
14“Ran da na hukunta mutanenIsra'ila saboda zunubansu,Zan hallakar da bagadan Betel.Za a kakkarya zankayen bagaden,Su fāɗi ƙasa.
15Zan murmushe gidajensu na rani dana damuna.Zan hallakar da gidajen da akaƙawata da hauren giwa,Kowane babban gida kuwa za arushe shi.”