Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
16 verses
1Ubangiji ya ce,“Mutanen Mowab sun ci gaba dayin zunubi.Hakika, zan hukunta su,Don sun ƙone ƙasusuwan SarkinEdomDon su yi toka da su.
2Zan aukar da wuta a ƙasarMowab,Ta ƙone kagarar Keriyot.Jama'ar Mowab za su mutu ahargitsin yaƙi,Sa'ad da sojoji suke sowa, ana busaƙahoni.
3Zan kashe Sarkin Mowab dashugabannin ƙasar.”
4Ubangiji ya ce,“Mutanen Yahuza sun ci gaba da yinzunubi.Hakika, zan hukunta su,Don sun raina koyarwata sun ƙibin umarnaina.Allolinsu na ƙarya waɗandakakanninsu suka bauta wa,Sun sa su su ratse daga hanya.
5Saboda haka zan aukar da wuta akan YahuzaTa ƙone kagarar Urushalima.”
6Ubangiji ya ce,“Mutanen Isra'ila sun ci gaba da yinzunubi.Hakika, zan hukunta su,Don sun sayar da salihai waɗandasuka kāsa biyan bashinsu.Sun kuma sayar da matalautaWaɗanda bashinsu bai kai ko kuɗinbi- shanu ba.
7Sun tattake marasa ƙarfi dakāsassu,Suna tunkuɗe matalauta su wuce.Tsofaffi da samari sukan tafi wurinkaruwan Haikali.Ta haka suke ɓata sunana maitsarki.
8A duk wuraren sujadarsu sukankwantaA bisa tufafin da suka karɓe jingina.A cikin Haikalin Allahnsu, sukan sharuwan inabiDa suka karɓo daga wurin waɗandasuke bi bashi.
9“Amma ga shi, saboda ku nahallakar da Amoriyawa,Dogayen mutanen nan masu kamada itatuwan al'ul,Ƙarfafa kuma kamar itatuwan oak,Na hallaka su ƙaƙaf.
10Na fito da ku, wato jama'ata dagaMasar.Na bi da ku cikin jeji shekaraarba'in,Na kuwa ba ku ƙasar Amoriyawa tazama taku.
11Na zaɓi waɗansu daga cikin'ya'yanku su zama annabawa,Waɗansu kuma daga cikin samarinkusu zama keɓaɓɓu.Ko ba haka ba ne, ya kuIsra'ilawa?Ni, Ubangiji, na yi magana.
12Amma kun sa keɓaɓɓu shan ruwaninabi,Kuka kuma umarci annabawa kadasu isar da saƙona.
13Zan danƙare ku a inda kukeKamar yadda ake danƙareamalanke da kayan tsaba.
14Ko masu saurin gudu ma ba za sutsere ba,Ƙarfafa za su zama kumamai,Sojoji kuma ba za su iya ceton kansuba.
15'Yan baka ba za su iya ɗagewa ba.Masu saurin gudu ba za su tsira ba.Mahayan dawakai kuma ba za sutsere da rayukansu ba.
16Ko sojojin da suka fi jaruntaka dukama,Za su gudu tsirara a ran nan.”Ubangiji ne ya faɗa.