Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
15 verses
1Ga zantuttukan Amos, ɗaya daga cikin makiyayan ƙauyen Tekowa. Allah ya bayyana wa Amos wannan saƙo, tun shekara biyu kafin girgizar duniya, a lokacin da Azariya yake sarautar Yahuza, Yerobowam ɗan Yehowash kuwa yake sarautar Isra'ila.
2Amos ya ce,“Ubangiji zai yi ruri daga Sihiyona,Muryarsa za ta yi tsawa dagaUrushalima.Da jin wannan, sai wuraren kiwo zasu bushe,Ƙwanƙolin Dutsen Karmel, da yakekore zai yi yaushi.”
3Ubangiji ya ce,“Mutanen Dimashƙu sun ci gaba dayin zunubi.Hakika, zan hukunta su,Don sun zalunci mutanen Gileyad dazalunci mai tsanani.
4Don haka zan aukar da wuta a kanfādar Sarkin Suriya.Za ta ƙone kagarar Ben-hadad,sarki.
5Zan ragargaje ƙyamaren ƙofofinbirnin Dimashƙu,In kawar da masu sarautar Bet-edenda na kwarin Awen.Za a kwashe mutanen Suriya ganimazuwa ƙasar Kir.”
6Ubangiji ya ce,“Mutanen Gaza sun ci gaba da yinzunubi.Hakika, zan hukunta su,Don sun kwashe al'umma duka, sunsayar wa mutanen Edom.
7Saboda haka zan aukar da wuta akan garun Gaza ta ƙone kagararbirnin.
8Zan kawar da masu sarautar biranenAshdod da Ashkelon,Zan karɓe sandan mulkin Ekron.Sauran Filistiyawa da suka ragukuma,Za su mutu duka.”
9Ubangiji ya ce,“Mutanen Taya sun ci gaba da yinzunubi.Hakika, zan hukunta su,Don sun kwashe mutanen sun kaiƙasar Edom.Suka karya yarjejeniyar abuta waddasuka yi.
10Saboda haka zan aukar da wuta akan garun Taya,Ta ƙone kagarar birnin.”
11Ubangiji ya ce,“Mutanen Edom sun ci gaba da yinzunubi.Hakika, zan hukunta su,Don sun farauci 'yan'uwansu,Isra'ilawa,Suka ƙi su nuna musu jinƙai.Ba su yarda su huce daga fushinsuba.
12Saboda haka zan aukar da wuta akan Teman,Ta ƙone kagarar Bozara.”
13Ubangiji ya ce,“Mutanen Ammon sun ci gaba da yinzunubi.Hakika, zan hukunta su,Don haɗamarsu ta ƙasa,Suka tsaga mata masu ciki aGileyad.
14Saboda haka zan aukar da wuta akan garun Rabba,Ta ƙone kagarar birnin.Za a yi kururuwa a ranar yaƙi,Faɗan kuwa zai yi rugugi kamarhadiri.
15Sarkinsu da manyan mutanensu za akai su wata ƙasa dabam.”