Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
21 verses
1“A wannan lokaci zan mayar waYahuza da Urushalima dawadatarsu.
2Zan tattara dukan al'ummai,In kai su kwarin Yehoshafat.A can zan yi musu shari'aA kan dukan abin da suka yi wajama'ata.Sun warwatsa Isra'ilawa a sauranƙasashe,Suka rarraba ƙasata.
3Sun jefa kuri'a a kan mutanena,Sun sayar da yara, mata da maza,zuwa bautaDon su biya karuwai da ruwaninabi.
4“Taya da Sidon, da dukan Filistiya, me kuke so ku yi mini? Kuna ƙoƙari ku rama mini saboda wani abu? Idan haka ne, zan rama muku da gaggawa.
5Kun kwashe azurfata da zinariyata kun kuma washe taskata, kun kai cikin haikalinku.
6Kun kwashe mutanen Yahuza da Urushalima, kun kai su nesa da ƙasarsu, sa'an nan kun sayar da su ga Helenawa.
7Yanzu zan dawo da su daga wuraren da kuka sayar da su, zan yi muku abin da kuka yi musu.
8Zan sa a sayar wa mutanen Yahuza 'ya'yanku mata da maza, su kuma za su sayar da su ga Sabiyawa, can nesa. Ni Ubangiji na faɗa.”
9Ku sanar wa al'ummai da wannan,Su yi shirin yaƙi,Su kira mayaƙa!Su tattaro sojoji, su zo!
10Su bubbuge allunan garmunansu,Su yi takuba da su.Su ƙera māsu da wuƙaƙen da akeyi wa itatuwa aski.Sai marar ƙarfi ya ce, “Ni jarumine!”
11Su gaggauta, su zo su al'ummai dasuke kewaye,Su tattaru a kwarin.“Ya Ubangiji, ka saukar darundunarka mai ƙarfi.”
12“Sai al'ummai su yi shiri,Su zo kwarin Yehoshafat,Gama a can zan zauna in shara'antaal'umman da suke kewaye,
13Su sa lauje gama hatsin ya isa girbi.Su shiga su tattaka,Gama wurin matsewar ruwan inabiya cika.Manyan randuna sun cika sunatumbatsa,Gama muguntarsu da yawa take.”
14Dubun dubbai suna cikin kwarin daza a yanke shari'a!Gama ranar Ubangiji ta kusa zuwa akwarin yanke shari'a.
15Rana da wata sun yi duhu,Taurari kuma ba su haskakawa.
16Ubangiji yana magana da ƙarfi dagaSihiyona,Yana tsawa daga Urushalima,Sammai da duniya sun girgiza.Amma Ubangiji shi ne mafakarjama'arsa, Shi ne kagarar mutanen Isra'ila.
17“Sa'an nan za ku sani ni ne UbangijiAllahnku,Wanda yake zaune a Sihiyona, tudunatsattsarka.Urushalima kuma za ta tsarkaka,Sojojin abokan gāba ba za su ƙararatsawa ta cikinta ba.
18“A wannan lokaci tsaunuka za su rufuda kurangar inabi,Tuddai za su cika da shanu,Dukan rafuffukan Yahuza za sugudano da ruwa,Maɓuɓɓuga za ta gudano dagaHaikalin Ubangiji,Ta shayar da kwarin Shittim.
19“Masar za ta zama hamada,Edom kuma za ta zama kufai,Saboda kama-karya da suka yi wamutanen Yahuza,Saboda sun zubar da jinin marasalaifi a ƙasarsu,
20Za a zauna a Yahuza da Urushalimadukan tsararraki har abada.
21Zan sāka alhakin jininsu,Ba zan kuɓutar da mai laifi ba,Gama Ubangiji yana zaune a Sihiyona.”