Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
19 verses
1Maganar Irmiya ɗan Hilkiya ke nan, na cikin firistocin da suke a Anatot, a yankin ƙasar Biliyaminu,
2wanda Ubangiji ya yi masa magana a zamanin Yosiya ɗan Amon, Sarkin Yahuza, a shekara ta goma sha uku ta mulkinsa,
3da a zamanin Yehoyakim ɗan Yosiya Sarkin Yahuza kuma, har ƙarshen shekara ta goma sha ɗaya ta Zadakiya ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, har zuwa lokacin da aka kai mazaunan Urushalima zaman talala a wata na biyar.
4Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
5“Na san ka tun kafin a yi cikinka,Na keɓe ka tun kafin a haife ka,Na sa ka ka zama annabi gaal'ummai.”
6Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah!Ban san abin da zan faɗa ba,Gama ni yaro ne.”
7Amma Ubangiji ya ce mini,“Kada ka ce kai yaro ne,Kai dai ka tafi wurin mutanen da zanaike ka,
8Kada ka ji tsoronsu, gama ina tare dakai,Zan kiyaye ka.Ni Ubangiji na faɗa.”
9Sa'an nan Ubangiji ya miƙa hannunsa ya taɓa bakina, ya ce mini,“Ga shi, na sa maganata a bakinka.
10Ga shi, a wannan rana na ba ka iko akan al'ummai da mulkoki,Don ka tumɓuke, ka rusar,Ka hallakar, ka kaɓantar,Ka gina, ka dasa.”
11Sai Ubangiji ya tambaye ni, ya ce, “Irmiya, me ka gani?”Na amsa, na ce, “Sandan itacen almond.”
12Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Ka gani sosai, gama zan lura da maganata don in cika ta.”
13Ubangiji ya sāke yi mini magana ya ce, “Me kuma ka gani?”Na ce, “Na ga tukunya tana tafasa, daga wajen arewa kamar za ta jirkice wajen kudu.”
14Sai Ubangiji ya ce mini, “Daga wajen arewa masifa za ta fito ta auka wa dukan mazaunan ƙasar.
15Ga shi kuwa, ina kiran dukan kabilan mulkokin arewa, za su kuwa zo su kafa gadajen sarautarsu a ƙofofin Urushalima, su kewaye dukan garukanta da dukan sauran biranen Yahuza.
16Zan hurta hukuncin da zan yi musu saboda dukan muguntarsu, da suka bar bina, suka ƙona turare ga gumaka, suka kuma bauta wa gumakan da suka yi.
17Amma kai, ka tashi ka sha ɗamara, ka faɗa musu dukan abin da na umarce ka. Kada ka ji tsoronsu domin kada in tsoratar da kai a gabansu.
18Ni kuwa, ga shi, yau na maishe ka birni mai kagara, da ginshiƙin ƙarfe, da bangon tagulla ga dukan ƙasar, da sarakunan Yahuza, da shugabanninta, da firistocinta, da mutanen ƙasar.
19Za su yi gāba da kai, amma ba za su ci nasara a kanka ba, gama ina tare da kai, ni Ubangiji na faɗa.”