Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
37 verses
1Ubangiji ya ce mini,
2in tafi in yi shelar abin da Ubangiji ya ce a kunnen Urushalima, in ce,“Na tuna da amincinki a lokacinƙuruciyarki,Da ƙaunarki kamar ta amarya daango.Yadda kika bi ni a cikin jeji, da aƙasar da ba a shuka ba.
3Isra'ila tsattsarka ce ta Ubangiji,Nunar fari ta girbina.Dukan waɗanda suka ci daga cikinkisun yi laifi,Masifa za ta auko miki.Ni Ubangiji, na faɗa.”
4Ku ji jawabin Ubangiji, ku zuriyar Yakubu, ku dukan kabilan Isra'ila.
5Ubangiji ya ce,“Wane laifi ne na yi wa kakanninku,Da suka bar bina?Suka bauta wa gumaka marasaamfani,Su kuma suka zama marasa amfani.
6Ba su kula da ni ba,Ko da yake na cece su daga ƙasarMasar.Na bi da su a cikin hamada,A ƙasa mai tuddai da kwazazzabai,Busasshiya mai yawan hatsari,Ba a bi ta cikinta,Ba wanda yake zama cikinta kuma.
7Na kawo su zuwa ƙasa mai dausayi,Don su more ta su ci amfaninta,Amma da suka shiga, sun ƙazantarmini da ita,Suka sa ƙasar da na gādar musu tazama abar ƙyama.
8Firistoci kuma ba su ce, ‘Ina Ubangiji Yake’ ba?Masanan shari'a ba su san ni ba.Masu mulki sun yi mini laifi,Annabawa sun yi annabci da sunanBa'al,Sun bi waɗansu abubuwa marasaamfani.”
9“Domin haka, ni Ubangiji zangabatar da ku gaban shari'a.Ku da 'ya'yanku, da 'ya'yan'ya'yanku, wato jikokinku.
10Ku haye zuwa tsibirin Kittim wajenyamma, ku gani,Ku aika zuwa Kedar wajen gabas, kuduba da kyau,A dā an taɓa yin wani abu haka?
11Akwai wata al'umma da ta taɓasāke gumakantaKo da yake su ba kome ba ne?Amma mutanena sun sauya darajarsuda abin da ba shi da rai.
12Sammai, ku girgiza saboda wannan,ku razana,Ku yi shiru, ni Ubangiji na faɗa.
13Mutanena sun yi zunubi iri biyu,Sun rabu da ni, ni da nakemaɓuɓɓugar ruwan rai,Sun haƙa wa kansu tafkunan ruwa,hudaddu,Waɗanda ba za su iya ajiye ruwa ba.
14“Isra'ila ba bawa ba ne, ba a kumahaife shi bawa ba,Amma me ya sa ya zama ganima?
15Zakuna suna ruri a kansa,Suna ruri da babbar murya.Sun lalatar da ƙasarsa,Garuruwansa sun lalace,Ba wanda yake zaune cikinsu.
16Mutanen Memfis kuma da naTafanes sun fasa ƙoƙwan kansa.
17Ya Isra'ila, kai ne ka jawo wa kankawannan,Da ka rabu da Ubangiji Allahnka,Sa'ad da ya bishe ka a hanya.
18Wace riba ka samu, har da ka tafiMasar,Don ka sha ruwan Kogin Nilu?Wace riba ka samu, har da ka tafiAssuriya,Don ka sha ruwan KoginYufiretis?
19Muguntarka za ta hore ka,Riddarka kuma za ta hukunta ka.Sa'an nan za ka sani, ka kumagane,Ashe, mugun abu ne, mai ɗaci, a garekaKa rabu da Ubangiji Allahnka,Ba ka tsorona a zuciyarka.Ni Ubangiji, Allah Mai Runduna nafaɗa.”
20“Ya Isra'ila, tun da daɗewa, ka ƙiyardaUbangiji ya mallake ka,Ka ƙi yin biyayya da ni,Ka kuwa ce, ‘Ba zan yi bauta ba.’Amma ka yi karuwanci a kankowane tudu,Da kowane ɗanyen itace.
21Na dasa ka kamar zaɓaɓɓiyarkurangar inabi, zaɓaɓɓen iri mafikyau.Ta yaya ka lalace haka ka zamarassan kurangar inabi ta jeji,Waɗanda ba zan yarda da su ba?
22Ko da za ka yi wanka da sabulunsalo,Ka yi amfani da sabulu mai yawa,Duk da haka zan ga tabbanzunubanka.Ni Ubangiji Allah na faɗa.
23Ƙaƙa za ka ce ba ka ƙazantar dakanka ba,Ba ka taɓa bin gunkin nan Ba'al ba?Ka duba hanyarka ta zuwa cikinkwari, ka san abin da ka yi.Kana kama da taguwa, mai yawonneman barbara.
24Kamar jakar jeji kake, wadda takeson barbara,Wadda take busar iska,Sa'ad da take son barbara, wa zai iyahana ta?Jakin da take sonta, ba ya bukatarwahalar da kansaGama a watan barbararta za a sameta.
25Kai Isra'ila, kada ka bar ƙafafunkaba takalma,Kada kuma ka bar maƙogwaronkaya bushe.Amma ka ce, ‘Wannan ba amfani,Gama na ƙaunaci baƙi, su kuwazan bi.’
26“Kamar yadda ɓarawo yakan shakunya sa'ad da aka kama shi,Haka nan mutanen Isra'ila za su shakunya,Da su, da sarakunansu, dashugabanninsu,Da firistocinsu, da annabawansu.
27Waɗanda suka ce wa itace, ‘Kai nemahaifinmu.’Suna kuma ce wa dutse, ‘Kai, kahaife mu.’Gama sun ba ni baya, ba su fuskanceni ba.Amma sa'ad da suke shan wahala,sukan ce,‘Ka zo ka taimake mu.’
28Ina gumakan da kuka yi wakanku?Bari su tashi in sun iya cetonkulokacin wahalarku.Yahuza, yawan gumakanku sun kaiYawan garuruwanku.
29Ni Ubangiji, ina tambayarku, ‘Waceƙara kuke da ita game da ni?’Kun yi mini tawaye dukanku.
30Na hori 'ya'yanku, amma a banza, basu horu ba,Kun kashe annabawanku da takobikamar mayunwacin zaki.
31Ya ku mutanen zamanin nan, kusaurari maganata.Na zamar wa Isra'ila jeji? Ko ƙasarda take da kurama?Don me fa mutanena suke cewa,‘Mu 'yantattu ne,Ba za mu ƙara zuwa wurinka ba’?
32Budurwa ta manta da kayankwalliyarta?Ko kuwa amarya ta manta da kayanadonta?Amma mutanena sun manta da nikwanaki ba iyaka.
33Kun sani sarai yadda za ku yi kufarauci masoya,Har mugayen mata ma, kun koyamusu hanyoyinku.
34Tufafinku sun ƙasantu da jininmarasa laifi,Waɗanda ba ku same su suna fasagidajenku ba.Amma duk da haka kuna cewa,
35‘Ba mu da laifi, hakika kuwa,Ubangiji bai yi fushi da mu ba.’Amma ni Ubangiji zan hukunta ku,Domin kun ce ba ku yi zunubi ba.
36Me ya sa ba ku da tsayayyiyar zuciya,Sai ku yi nan ku yi can?Masar za ta kunyata ku kamar yaddaAssuriya ta yi.
37Da hannuwanku a kā za ku komodaga Masar don kunya.Gama waɗanda kuke dogara gare su,ni Ubangiji, na ƙi su,Ba za ku yi arziki tare da su ba.”