Loading Bible Translation
First-time download in progress. This may take a few seconds…
Hausa Holy Bible Wordproject Bible
25 verses
1Ubangiji ya ce,“Idan mutum ya saki matarsa,Ta kuwa rabu da shi, har ta auriwani,Ya iya ya komo da ita?Ashe, yin haka ba zai ƙazantar daƙasar ba?Ya Isra'ila, kin yi karuwanci,Abokan sha'anin karuwancinki, sunada yawa.Za ki sāke komowa wurina?Ni, Ubangiji, na faɗa.
2Ki ta da idonki, ki duba filayentuddai ki gani,Akwai wurin da ba ki laɓe kin yikaruwanci ba?Kin yi ta jiran abokan sha'aninkaruwancinki a kan hanya,Kamar Balaraben da yake fako ahamada.Kin ƙazantar da ƙasar da mugunkaruwancinki.
3Saboda haka aka ƙi yin ruwa,Ruwan bazara bai samu ba.Goshinki irin na karuwa ne, ba ki jinkunya.
4“Yanzu kin ce, ‘Kai ne mahaifina,Ka ƙaunace ni tun ina cikinƙuruciyata.
5Za ka dinga yin fushi da ni?Za ka husata da ni har abada?’Ga shi, ke kika faɗa, amma ga shi,kin aikata dukan muguntar dakika iya yi.”
6A zamanin sarki Yosiya, Ubangiji ya ce mini, “Ka ga abin da take yi, ita marar amincin nan, wato Isra'ila? Yadda a kowane tudu mai tsayi, da a gindin kowane itace mai duhuwa, a wurare ne ta yi karuwancinta.
7Na yi zaton bayan da ta aikata wannan duka, za ta komo wurina. Amma ba ta komo ba, maƙaryaciyar 'yar'uwarta, wato Yahuza, ta gani.
8Yahuza kuwa ta ga dukan karuwancin da marar amincin nan, Isra'ila ta yi, na sake ta, na ba ta takardar sarki. Amma duk da haka maƙaryaciyar 'yar'uwan nan tata, Yahuza, ba ta ji tsoro ba, amma ita ma ta tafi ta yi karuwanci.
9Domin karuwanci a wurinta abu ne mai sauƙi, ta ƙazantar da ƙasar. Ta yi karuwanci da duwatsu, da itatuwa.
10Duk da haka maƙaryaciyar 'yar'uwan nan tata, Yahuza ba ta juyo wurina da zuciya ɗaya ba, sai a munafunce, ni Ubangiji na faɗa.”
11Ubangiji kuma ya faɗa mini, ko da yake Isra'ila ta bar binsa, duk da haka ta nuna laifinta bai kai na Yahuza marar aminci ba.
12Ya ce mini in tafi wajen arewa in yi shela in ce,“Ki komo ya Isra'ila, marar aminci,Ni Ubangiji, na faɗa.Domin ni mai jinƙai ne,Ba zan yi fushi da ke ba.Ba zan yi fushi da ke har abada ba,Ni, Ubangiji na faɗa.
13Ke dai ki yarda da laifinki,Da kika yi wa Ubangiji Allahnki,Kin kuma watsar da mutuncinki awurin baƙiA gindin kowane itace mai duhuwa.Kika ƙi yin biyayya da maganata,Ni, Ubangiji, na faɗa.
14“Ku komo, ya ku mutane marasaaminci,Gama ni ne Ubangijinku.Zan ɗauki mutum guda daga kowanegari,In ɗauki mutum biyu daga kowaneiyali,Zan komo da su zuwa DutsenSihiyona.
15Zan ba ku sarakuna waɗanda suke yi mini biyayya da hikima da fahimi.
16Sa'ad da kuka yawaita a ƙasar, mutane ba za su ƙara yin magana a kan akwatin alkawari na Ubangiji ba. Ba za su ƙara yin tunaninsa ko su tuna da shi, ko su bukace shi, ko kuwa su yi wani irinsa ba.
17In lokacin nan ya yi, za a kira Urushalima gadon sarautar Ubangiji, dukan sauran a'umma za su taru a Urushalima da sunana. Ba za su ƙara bin tattaurar zuciyarsu mai mugunta ba.
18A waɗannan kwanaki mutanen Yahuza za su haɗu da mutanen Isra'ila. Tare za su zo daga ƙasar arewa zuwa cikin ƙasar da na ba kakanninku gādo.”
19“Isra'ila, na yi niyya in karɓe kukamar ɗana,In gādar muku da kyakkyawarƙasaMafi kyau a dukan duniya.Na zaci za ku ce ni ne mahaifinku,Ba za ku ƙara rabuwa da bina ba.
20Hakika kamar yadda mace mararaminci takan bar mijinta,Haka kun zama marar aminci a gareni, ya jama'ar Isra'ila.Ni Ubangiji, na faɗa.”
21An ji murya a kan filayen tuddai,Kūka da roƙo ne na 'ya'yanIsra'ila maza,Domin sun rabu da hanyarsu,Sun manta da Ubangiji Allahnsu.
22“Ku juyo ku marasa aminci,Zan warkar da rashin amincinku.“To, ga shi, mun zo gare ka,Gama kai ne Ubangiji Allahnmu,
23Daga kan tuddai ba mu da wanitaimako,Ko daga hayaniyar da ake yi a kanduwatsu,Daga wurin Ubangiji Allahnmu nekaɗai taimakon Isra'ila yakefitowa.
24“Amma yin sujada ga gunkin nan Ba'al ya cinye mana amfanin wahalar da kakanninmu suka sha tun muna yara, wato na garkunan tumakinsu, da na awakinsu, da na shanunsu, da 'ya'yansu mata da maza.
25Bari mu kwanta mu sha kunyarmu, bari kuma rashin kirkinmu ya rufe mu. Gama mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi mu da kakanninmu, tun daga ƙuruciyarmu har zuwa yau, ba mu yi biyayya ga maganar Ubangiji Allahnmu ba.”